2023: Ku Gaggauta Gyara Kundin Tsarin Zaɓe, PDP Ga Shugaba Buhari Da APC

2023: Ku Gaggauta Gyara Kundin Tsarin Zaɓe, PDP Ga Shugaba Buhari Da APC

- Jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta bada umarnin fara gyaran kundin tsarin zaɓen ƙasar nan.

- Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Hedkwatar PDP dake Abuja.

- Shugaban yace yan Najeriya ba zasu yarda da duk wani tuggu da jam'iyya mai mulki zata kulla ba a zaɓen mai zuwa.

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar sa ta APC da su fara shirin gyaran kundin tsarin zaɓen ƙasar nan don tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a babban zaɓen dake tafe, 2023.

KARANTA ANAN: Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 16 da suka mutu kan mulki

Shugaban PDP na ƙasa, Uche Secundus, ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron da jami'iyyar ta gudananr ran Laraba, a Hedkwatar ta dake babban birnin tarayya, Abuja.

Uche ya ce:

"Muna kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar sa APC da su gabatar da gyaran tsarin gudanar da zaɓen ƙasar nan domin ganin anyi sahihin zaɓe a shekarar 2023 dake tafe, hakan zai sa Najeriya ta yi gogayya da sauran ƙasashen da suka cigaba, kamar ƙasar Ghana," a cewar shugaban na PDP."

2023: Ku Gaggauta Gyara Kundin Tsarin Zaɓe, PDP Ga Shugaba Buhari Da APC
2023: Ku Gaggauta Gyara Kundin Tsarin Zaɓe, PDP Ga Shugaba Buhari Da APC Hoto: @Officialpdpnig
Asali: Twitter

Ya kuma zargi shugaban da jam'iyyarsa mai mulki da shirya wata maƙarkashiya a zaɓen dake tafe, Uche ya gargaɗe su da cewa 'yan Najeriya ba zasu yarda da abinda suke shiryawa ba, Channels TV ta ruwaito.

Anashi ɓangaren shugaban kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP, Sanata Bukola Saraki, ya yi kira ga yan jam'iyyar da su haɗa kansu.

KARANTA ANAN: Da duminsa: Bayan watanni 6, Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya

"Ina ganin yakamata mu karfafa junan mu domin tunkarar ƙalubalen dake gaban mu, ƙalubale ne mai matuƙar wahala amma kada mu karaya," a cewar Saraki.

Sauran 'yayan jam'iyyar da suka halarci taron sun ƙarfafa maganar Saraki cewa akwai buƙatar su haɗa kansu sun zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, sannan a sanya matasa da mata a muƙamai daban-daban Idan har jam'iyyar naso ta ƙwace mulki a 2023.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta amince da siyo ma NCDC kayan aiki na Biliyan Uku

Majalisar zartarwar ƙasar nan ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta amince ta fidda kuɗi Naira biliyan uku don siyo kayayyakin gwaje-gwaje a hukumar NCDC

Ministan Lafiya, Osanigie Ehanire, ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron majalisar jiya Laraba.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262