Boko Haram Sun Tsinke Wutar Lantarkin Maiduguri, Mazauna Suna Fama da Kudin Fetur

Boko Haram Sun Tsinke Wutar Lantarkin Maiduguri, Mazauna Suna Fama da Kudin Fetur

- Jama'ar Maiduguri na fama da tsananin rashin wutar lantarki wanda hakan yasa farasin fetur yayi tashin gwauron zabi

- Garin ya fada cikin duhu ne tun bayan da 'yan Boko Haram suka lalata wuta sannan suka saka bama-bamai a inda ake gyaran

- A halin yanzu litar man fetur ta kai N450 zuwa N500 a hannun 'yan bumburutu wadanda kasuwarsu ta bude a garin

Kusan watanni biyu kenan da garin Maiduguri ke fama da matsanancin rashin wuta tun bayan da 'yan Boko Haram suka tsinke musu layikan rarrabe wutar lantarki tare da saka wa wasu wurare bama-bamai.

A yayin da aka fara gyara, 'yan ta'addan sun saka bama-bamai wadanda suka raunta jami'an kamfanin rarrabe wutar lantarki ta Najeriya.

Yayin da gyaran ke cigaba amma da taimakon sojojin da ke ba ma'aikatan kariya, mazauna yankin da 'yan kasuwa sun matukar dogara da man fetur wurin samun wuta.

Amma bayan rahotanni da suka bazu a makon da ya gabata kan farashin man fetur, bukatarsa ta tsananta a fadin babban birnin na jihar Borno.

KU KARANTA: Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

Boko Haram Sun Tsinke Wutar Lantarkin Maiduguri, Mazauna Suna Fama da Kudin Fetur
Boko Haram Sun Tsinke Wutar Lantarkin Maiduguri, Mazauna Suna Fama da Kudin Fetur. Hoto daga @Channelstv
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

Duk da gwamnatin tarayya ta musanta karin farashin, 'yan kasuwar man fetur sun fara boye shi, lamarin da yasa farashinsa ya tashi.

Mazauna yankin ballantana masu matukar bukatar wutar sun koma wurin 'yan bumburutu neman fetur.

"Lita daya ta man fetur a farko N200 take, amma a lokacin nan da babu shi, ana siyar da lita kan N450 ko N500," wani dan bumburutu mai suna Mohammed Abdulrahman ya sanar da Channels TV

"A gaskiya yanzu da babu fetur muna samun riba sosai. Amma a lokutan da akwai bamu samun kwastomomi. Wata rana sai ka samu mutum biyar zuwa shida kacal."

A wani labari na daban, shugaban hukumar NSCDC, Ahmed Audi yace 'yan bindigan da suka gallabi 'yan Najeriya suna da masu daukar nauyinsu daga kasashen ketare.

Audi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron horarwa na shugabannin jihohi da hukumar tayi a babban birnin tarayya, Abuja.

Taron horarwar wanda kamar yadda hukumar tace, an yi shi ne domin karfafa fannin shugabanci, mu'amala da kuma kwarewa wurin shawo kan tarzoma.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Online view pixel