Daga kasashen ketare ake daukar nauyin 'yan bindigan Najeriya, Shugaban NSCDC

Daga kasashen ketare ake daukar nauyin 'yan bindigan Najeriya, Shugaban NSCDC

- Ahmed Audi, shugaban hukumar NSCDC ya tabbatar da cewa akwai masu daukar nauyin 'yan bindiga a kasashen ketare

- Shugaban ya sanar da hakan ne a wani taron horarwa da hukumar tayi wa kwamandojinta na jihohi a Abuja

- Audi yace 'yan bindiga da suka gallabi Najeriya da gaske suke kuma ya zama dole hukumomin tsaro su hada kansu

Shugaban hukumar NSCDC, Ahmed Audi yace 'yan bindigan da suka gallabi 'yan Najeriya suna da masu daukar nauyinsu daga kasashen ketare.

Audi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron horarwa na shugabannin jihohi da hukumar tayi a babban birnin tarayya, Abuja.

Taron horarwar wanda kamar yadda hukumar tace, an yi shi ne domin karfafa fannin shugabanci, mu'amala da kuma kwarewa wurin shawo kan tarzoma.

Channels TV ya ruwaito cewa, Audi yace kasar nan na fuskantar babban kalubale, hakan ne yasa ake bukatar hadin kai daga hukumomin tsaro.

KU KARANTA: Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya

Daga kasashen ketare ake daukar nauyin 'yan bindigan Najeriya, Shugaban NSCDC
Daga kasashen ketare ake daukar nauyin 'yan bindigan Najeriya, Shugaban NSCDC. Hoto daga @ChannelsTv
Source: Twitter

"Biyo bayan al'amuran dake faruwa a kasar nan, muna fuskantar tarzomar da a tarihin kasar nan bamu taba gani ba.

"Mun taba fuskantar makamantan wadannan tashin hankulan a kasar nan, amma ba sak ba. Wannan al'amarin yana bukatar hukumomin tsaro su hada karfi da karfe wurin kawo karshensa.

"Wadannan mutanen sun dage, wadannan mutanen na da masu daukar nauyinsu daga kasashen ketare. Don haka dole ne mu hada kanmu," shugaban yace.

KU KARANTA: An kama tsohon dan gidan fursuna da aka yi wa rangwame yana siyar da miyagun makamai ga 'yan ta'adda

A wani labari na daban, rahotanni dake zuwa daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar nan na nuna cewa miyagun 'yan bindiga sun halaka mutum takwas, ciki har da sojoji uku bayan wata arangama da suka yi.

Hakazalika, wasu mutum bakwai da suka matukar jigata suna asibiti inda suke samun taimakon likitoci sakamakon hari da 'yan bindigan suka kai a kauyen a ranar Talata.

Mummunan labarin na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da 'yan bindiga suka kaiwa Sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Idris Maigwari II hari.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel