Rufe Boda Bai Hana Shigo Da Makamai Ba Bisa Ƙa'ida Ba, Shugaba Buhari

Rufe Boda Bai Hana Shigo Da Makamai Ba Bisa Ƙa'ida Ba, Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya yarda da cews rufe boda d gwamnatin sa tayi bai hana shigo da makamai ba bisa Ƙa'ida ba

- A shekarar 2019, Gwmnatin Buhari ta bayyana kulle dukkan bodar shigowa Najeriya ta ƙasa domin hana aikin fasa kwauri a ƙasar.

- Saidai a watan Disamban shekarar da ta gabata 2020, Gwamnatin ta sake buɗe bodar ta saboda yarjejeniyar da ta shiga ta kasuwanci da sauran ƙasashen Africa

Shugaban Ƙasa, mejo janar Muhammadu Buhari ya amince da cewa, duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa tayi na rufe boda a ƙasar nan hakan bai hana shigo da makamai cikin ƙasar nan ba bisa ƙa'ida ba.

Sai dai shugaban ya siffanta faruwar hakan da yanayin da ƙasar Libya take ciki, ya ce matukar Libya zata cigaba da kasancewa a halin da take ciki, to lallai haramtattun makamai da harsasai da sauran su zasu cigaba da kwarara yankin Sahel.

KARANTA ANAN: Gwamnatin tarayya ta amince da siyo ma NCDC kayan aiki na Biliyan Uku

A bayanin mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina, yace Shugaban ya yi jawabi ne lokacin da ya karɓi bakuncin wakilan UN, shugaban UN da sakataren sa na Africa, lokacin da sukazo yin bankwana a fadar shugaban ƙasa, Villa, dake Abuja.

Bayanin shugaban da akayi wa take da 'Rikicin Libya ne babbar matsalar kasasheɓ yankin Sahara, inji shugaba Buhari.'

Idan zaku iya tunawa, Najeriya ta kulle bodar ta a watan Augustan shekarar 2019 da zummar daƙile fasa kwauri a ƙasar.

Sai dai, an buɗe bodar a watan Disamba 2020 saboda aiwatar da yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen Africa wadda ta fara aiki 1 ga watan Janairu, 2021.

Rufe Boda Bai Hana Shigo Da Makamai Ba Bisa Ƙa'ida Ba, Shugaba Buhari
Rufe Boda Bai Hana Shigo Da Makamai Ba Bisa Ƙa'ida Ba, Shugaba Buhari Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito shugaba Buhari na cewa:

"Mun rufe bodar mu ta ƙasa na tsayon shekara ɗaya, amma makamai d sauran makamantansu sun cigaba da kwarara cikin ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Matuƙar Libya zata cigaba da kasan cewa cikin rikici to matsalolin mu ba zasu ƙare ba."

"Ya kamata mu jure waɗan nan matsalolin, amma da sannu za muga bayan su gaba ɗaya," a cewarsa.

KARANTA NAN: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari

Shugaban yace tsohon shugaban Libya, Muammar Gaddafi ya ɗauki masu gadinsa daga wasu ƙasasheɓ duniya, waɗan da suka tsere da makamansu bayan anka bayan shugaban.

"Basu san komai ba illa suyi harbi ko su yi kisa, sune matsalar mu a yankin sahara, Africa" inji Buhari.

Ya bayyana shuwagabannin da suka zo masa bankwana, waɗan da suka kwashe shekaru da yawa a ƙasar da cewa suma 'yan Najeriya ne. Ya kuma yi musu fatan Alkhairi.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun harbe wani matashi, sun yi awon gaba da Uwa da Ɗanta a Jigawa

Mutanen da ba'a san ko su waye ba sun harbi mutum ɗaya sun kuma yi awon gaba da mahaifiyarsa da ɗan uwansa

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ɗauki matakin gaggawa kamar yadda me magana da yawun ta ya faɗa

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262