Gwamnatin tarayya ta amince da siyo ma NCDC kayan aiki na Biliyan Uku

Gwamnatin tarayya ta amince da siyo ma NCDC kayan aiki na Biliyan Uku

- Majalisar zartarwar ƙasar nan ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta amince ta fidda kuɗi Naira biliyan uku don siyo kayayyakin gwaje-gwaje a hukumar NCDC

- Ministan Lafiya, Osanigie Ehanire, ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron majalisar jiya Laraba.

- Ya bayyana cewa aikin zai matukar taimakawa NCDC wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata

Gwamnatin tarayya ta amince ta fidda kuɗi Naira Biliyan uku domin siyo kayan aikin ɗakin gwaje-gwajen Hukumar NCDC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: 'Yan Majalisar Wakilai Sun Gayyaci Ministan Buhari Yazo Ya Musu Cikakken Bayani

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana haka jiya Laraba bayan fitowa daga taron majalisar zartarwa (FEC) wanda shugaba Buhari ke jagoranta.

Ministan yace: "Ma'aikatar lafiya ta gabatar da bukatar a gaban majalisar zartarwa a madadin NCDC."

Gwamnatin tarayya ta amince da siyo ma NCDC kayan aiki na Biliyan Uku
Gwamnatin tarayya ta amince da siyo ma NCDC kayan aiki na Biliyan Uku Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

"Kwangila ce guda shida na siyo kayayyaki daban-daban a ɗakin kwaje-gwaje wanda zai laƙume kuɗi kimanin N3,070,892,988 har da dakon su. Za'a siyo kayayyakin ne domin ƙara ƙarfafa aikin hukumar NCDC a fanni daban-daban." inji ministan.

KARANTA ANAN: Atiku, Kwankwaso za su iya kai labari, PDP ta fadi yadda za ta fitar da ‘Dan takarar 2023

Ya kuma ƙara da cewa: "Kayayyakin zasu taimaka musu wajen gudanar da dukkan ayyukan su, bawai COVID19 kaɗai ba, harda sauran cututtuka da ka iya ɓarkewa nan gaba."

Haka zalika, Ministan ayyukan gidaje, Babatunde Fashola, ya ce majalisar ta amince da aikin babbar hanyar Enugu zuwa Onitcha wanda zai laƙume N8.65bn.

A wani labarin kuma Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

Gwamnan yace kamata yayi a farko Gumi yayi musu wa'azi kan illar, fyade, sata, fashi, garkuwa da mutane da sauransu

Masari yace kwata-kwata salon Gumi ba zai kawo mafita ba ga rashin tsaron da ya addabi kasar nan ba.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262