Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki

Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki

- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi alkawarin yin biyayya ga bukatun mutanen da yake mulka

- Makinde ya nesanta kansa da iyayen gida a siyasa

- Gwamnan na Oyo ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata a dauki zaben shugaban kasa na 2023 a matsayin mai mahimmanci ba yanzu

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce zai sauka daga mukaminsa idan mutanen jihar suka nemi ya yi hakan.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba, 17 ga Maris, a taron kungiyar datawan Yarbawa da aka yi a Mapo Hall, Ibadan, PM News ta ruwaito.

Makinde ya ce shi bai damu da matsayin ba, inda ya kara da cewa shi ya sa ya lashi takobin yanke hukunci don amfanin jihar da kasar Yarbawa.

Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki
Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jerin Jihohin da ke da Mafi Yawa da Karancin Rashin Aikin Yi a Nigeria

Ya ce:

"Idan mutanen jihar Oyo suka nemi na bar ofis a matsayin gwamna a yau, ba zan yi jinkirin barin ofishin ba saboda a kullun da jakata nake zuwa ofis."

“Na tsaya takara a 2007, 2011 da 2015 amma na fadi kuma da lokaci ya yi da Allah Ya sa zan zama gwamna, shi ya sanya ni. Idan mutanen jihar suka yanke hukuncin cewa ba sa sona kuma, zan dauki jakata ne kawai in tafi saboda ba ni da ko allura a ofis.”

Makinde ya kuma bayyana cewa bashi da ubangidan siyasa sai Allah uba.

Da yake magana kan zaben shugaban kasa na 2023, gwamnan ya shawarci yankin kudu maso yamma da kada su mayar da hankali kan zaben da za a yi nan gaba yanzu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano

A cewar jaridar The Cable, ya ce ya kamata yankin ya fi mayar da hankali wajen ganin an yi adalci ga wadanda aka cuta.

Makinde wanda shine gwamna daya tilo a karkashin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a kudu maso yamma ya yi kira ga hadin kai don magance matsalar rashin tsaro a yankin.

A wani labari na daban, Jam'iyya mai mulki APC tayi zazzafan martani ga jam'iyyar hamayya ta PDP inda ta bayyana cewa cin hanci da rashawa da yama PDP katutu ne maƙasudin barin ta mulki a babban zaben 2015.

A ranar Talatan da ta gabata, sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP ya ce rahoton da hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa ba abinda jam'iyya mai mulki keyi sai yaudarar 'yan Najeriya da sunan samar musu da aikin yi.

Sakataren yace ashe duk yaudara ce kurin da APC da shugaba Buhari ke yi na samar da aiki ga 'yan Najeriya, Dailytrust ta ruwaito.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng