Rikicin Hijabi: Ba zamu yarda da duk wani yunƙurin CAN ba, Inji MURIC

Rikicin Hijabi: Ba zamu yarda da duk wani yunƙurin CAN ba, Inji MURIC

- Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su waiwayi abinda ke faruwa a Jihar Kwara.

- Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya bayyana cewa CAN ta ki bin umarnin da kotunan jihar Kwara suka bayar na barin musulmai su saka Hijabi

- An dai samu barkewar rikici a makarantar sakandiren Baptist dake Surulere, Illorin, tsakanin musulmai da kiristoci

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmai (MURIC) tace kwata-kwata ƙungiyar kiristocin Nijeriya ba ta koyi da tarihi.

Lokacin da yake martani ga rikicin dake faruwa a jihar Kwara na amfani da Hijabi a wasu daga cikin makarantun sakandiren jihar, shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya zargi CAN da rura wutar rikicin, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

Rikici ya ɓarke a makarantar sakandiren Baptist dake Surulere, Ilorin, Babban birnin jihar Kwara ran Laraba kan ƙin amince wa da hukumar makarantar ta yi ɗalibai mata musulmai su saka Hijabi.

Iyayen ɗaliban sun shiga zazzafar takaddama da hukumar makarantar har takai ga anfara jifa da dutse tsakanin kiristoci da Musulmai.

A jawabinsa, shugaban MURIC ya ce yana mamakin yadda shugabannin kiristocin suka ƙi suyi biyayya ga umarnin da kotu ta bayar akan lamarin.

"Muna mamakin yadda mutanen da ke ikirarin su wayayyu ne amma basu girmama doka. CAN ya kamata a zarga akan duk abinda ke faruwa. CAN ke ba mambobinta umarnin su zauna a wannan makarantar. Sai dai matsalolin na faruwa ne a ɗaya daga cikin makarantu 10, amma wannan babban abun kunya ne ga Jihar Kwara a ƙarni na 21 ace CAN na ziga 'yayan ta na fatali da doka a jihar," a cewar Akintola.

Rikicin Hijabi: Ba zamu yarda da duk wani yunƙurin CAN ba, Inji MURIC
Rikicin Hijabi: Ba zamu yarda da duk wani yunƙurin CAN ba, Inji MURIC Hoto: @thenationonline.net
Asali: UGC

Akintola ya kara da cewa:

"Babbar kotun Ilorin da kuma kotun ɗaukaka ƙara ta Ilorin sun bada umarni cewa yaran su saka Hijab. Saboda haka ba daidai bane, karya doka ne CAN ta sa 'yayanta su ƙi bin wannan umarnin kuma su dage baza'a bar dalibai musumai su saka hijab ba, ko harabar makarantar ma baza su shiga da hijab ba. Wannan babban laifi ne." inji shugaban MURIC.

Ya kara da cewa: "Mun tabbatar da CAN ke ɗaukar nauyin duk abinda ke faruwa a waɗannan makarantun. Muna mamakin yadda kungiyoyi a Najeriya sukai gum da bakin su akan wannan hawan ƙawara da ake ma doka. Saboda an maida musulmai koma baya? Ko kuma saboda CAN ne basu da gaskiya?

Bamu yarda da wannan rashin adalcin ba. Duk wanda ke son tabbatar da demokaraɗiyya dole su yi magana musamman lokacin da aka taɓa wani ginshiƙin demokaraɗiyya. Ƙin bin umarnin kotu bayyanannar adawa ce ga demokaraɗiyya da kuma kyakkywan shugabanci. Doka da zaman lafiya, ko kuma CAN na gaba da su ne?

KARANTA ANAN: FEC ta amince da aikin gyaran matatar man fetur dake Patakwal kan $1.5 biliyan

"Abun damuwar shine CAN ba sa koyi da tarihi. Umarnin da aka bayar a baya bayan nan ga ɗalibai Kisitoci su saka kayan cocin su a makaranta bazai yi nasara ba kamar yadda tafaru a Osun. Har na wane tsawon lokaci zasu saka irin waɗan nan kaya. Zamu gani damu dasu wazai bari." Inji shi

"Muna kira ga duk masu hankali a Najeriya da su duba abinda ke faruwa a jihar Kwara. Sanannen abu ne duk jama'ar dake irin wannan to suna gayyato hargitsi ne kawai. Kuma wannan shine abinda CAN ke ƙoƙarin yi. Saboda haka muna kira ga masu ruwa da tsaki da su dakatar da CAN."

"Muna kira ga gwamnatin jihar Kwara a kan jayayya da ikonta. Duk wani shiri da gwamanatin zata yi na goyon bayan CAN ko kuma danne haƙƙin musulmai wajen saka Hijabi, musulmai baza su yarda dashi ba, mun tsaya kan Hijab." shugaban MURIC ya fada

A wani labarin kuma Alkali ya yi wa EFCC kashedi, ya ja wa Lauyanta kunne a shari’ar Shehu Sani

Inyang Ekwo, Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya da ke garin Abuja , ya gargadi hukumar EFCC a wajen shari’ar da ake yi da Sanata Shehu Sani.

Alkali mai shari’a ya yi wannan kashedi ne bayan da lauyan wanda ake zargi, Abdul Ibrahim SAN, ya koka kan wani bayani da EFCC ta yi a shafinta na Twitter.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: