Cin Hanci Da Rashawa Ne Ya Raba Ku Da Mulki, APC Ta Maida Martani Ga PDP

Cin Hanci Da Rashawa Ne Ya Raba Ku Da Mulki, APC Ta Maida Martani Ga PDP

- Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan APC ta maida zazzafan martani ga babbar jam'iyyar adawa PDP bayan caccakar da tasha daga wajen PDP ɗin a kwanakin baya

- APC tace yawaitar cin hanci da rashawa yasa 'yan Najeriya suka juya ma PDP baya a zaben 2015

- A kwanakin baya ne jam'iyyar hamayya ta PDP ta caccaki APC da cewa ba abunda jam'iyyar ke yi sai tsantsar yaudara.

Jam'iyya mai mulki APC tayi zazzafan martani ga jam'iyyar hamayya ta PDP inda ta bayyana cewa cin hanci da rashawa da yama PDP katutu ne maƙasudin barin ta mulki a babban zaben 2015.

KARANTA ANAN: Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

A ranar Talatan da ta gabata, sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP ya ce rahoton da hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa ba abinda jam'iyya mai mulki keyi sai yaudarar 'yan Najeriya da sunan samar musu da aikin yi.

Sakataren yace ashe duk yaudara ce kurin da APC da shugaba Buhari ke yi na samar da aiki ga 'yan Najeriya, Dailytrust ta ruwaito.

Rahoton NBS ya bayyana cewa yawan marasa aikin yi a Najeriya ya karu zuwa 33%.

Cin Hanci Da Rashawa Ne Ya Raba Ku Da Mulki, APC Ta Maida Martani Ga PDP
Cin Hanci Da Rashawa Ne Ya Raba Ku Da Mulki, APC Ta Maida Martani Ga PDP Hoto: @ApcNigeria
Source: Facebook

Lokacin da yake martani, sakataren riko na jam'iyyar APC, Sen. John James yace gwamnatin su bata amince da duk wata kala na cin hanci da rashawa ba, a cikin gida ko a waje.

KARANTA ANAN: Boko Haram: Mun gaji haka; Sojoji sun roki sabon Hafsun Soji ya basu dama su ga iyalansu

"Najeriya ba tsibiri bane, mun sha wahala a tattalin arzikin mu saboda annobar COVID19 da ta addabi duniya, annobar ta taɓa rayuwar mu da aikin mu. amma duk da haka shugaba Buhari ya nuna iya shugabanci ta yadda ya fuskanci lamarin," inji sakataren APC.

Ya kuma kara da cewa: "Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fitar da kasar daga karayar tattalin arzikin data shiga saboda annobar korona."

A wani labarin kuma 'Yan Majalisar Wakilai Sun Gayyaci Ministan Buhari Yazo Ya Musu Cikakken Bayani

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika , ya bayyana a gabanta don ya mata bayanin tsaron da filayen jirgin sama ke dashi.

Majalisar tace ankai hare hare a filayen jirgin sama a Kaduna har an sace mutane 11.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit

Online view pixel