‘Yan bindiga sun hallaka wani ‘Dan kasuwa a kauyen Katsina, sun yi gaba da ‘ya ‘yansa

‘Yan bindiga sun hallaka wani ‘Dan kasuwa a kauyen Katsina, sun yi gaba da ‘ya ‘yansa

- ‘Yan bindiga sun shiga kauyen Jargaba cikin tsakar daren ranar Laraba

- Miyagun sun kashe wani mai Attajirin da ake ji da shi a yankin Bakori

- Bayan haka sun yi awon-gaba da ‘ya ‘ya biyu a gidan wannan mutumin

An samu wasu ‘yan bindiga sun shiga kauyen Jargaba da ke yankin karamar hukumar Bakori, jihar Katsina, sun yi ta’adi a cikin makon nan.

Rahoton da mu ka samu daga jaridar Katsina Post ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun hallaka wani ‘dan kasuwa mai suna Ibrahim Kwatahi.

Mutanen kauyen sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun kawo masu hari ne cikin dare a ranar Laraba, 17 ga watan Maris, 2021.

Da kimanin karfe 1:00 na tsakar dare wadannan miyagu su ka shigo kauyen Jargaba da kafa.

KU KARANTA: Arzikin Najeriya 'yan bindiga su ke kwadayi - Masari

Bayan hallaka wannan mashahurin ‘dan kasuwa a yankin na Bakori da ke Arewacin jihar Katsina, sun tsere da wasu ‘ya ‘ya biyu na marigayin.

Kamar yadda mu ka samu labari, an dauke ‘da da wata ‘diya da marigayin ya mutu ya bari.

Har ila yau, wadannan ‘yan bindiga da su ka dade su na ta’adi a yankin Katsina, sun sace kudi da ba a san adadinsu ba a gidan Alhaji Ibrahim Kwatahi.

Kawo yanzu da mu ke tattara rahoto, ba a samu labarin ‘yan bindigan sun tuntubi iyalin marigayin domin a biya kudin fansar yaran da aka sace ba.

‘Yan bindiga sun hallaka wani ‘Dan kasuwa a kauyen Katsina, sun yi gaba da ‘ya ‘yansa
Gwamna Aminu Masari Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Matakin da Masari ya dauka da aka sace Dalibai a Kankara

‘Yan sa-kai da su ka yi yunkurin bin ‘yan bindigan bayan sun yi aika-aikar da su ka yi, sun fahimci cewa an yi hanyar dajin Faskari ne da wadannan yara.

Karamar hukumar Faskari ya na cikin inda aka addaba, yankin ya na kan iyaka da jihar Zamfara.

Dazu kun ji wasu daga cikin sojojin kasan da su ke Arewa maso gabas sun nemi ayi sauyi, sun sike da yakin Boko Haram bayan shekaru biyar su na gwabza wa.

Akwai rundunar da za su yi azumin Ramadan na 6 a jere, ba tare da sun ga fuskokin iyalansu ba.

Sojojin sun roki sabon hafsun soji ya basu dama su ga 'yanuuwa da iyalansu, su ka ce a halin yanzu sun sare, kuma ba tunanin 'Yan Boko Haram ne a gabansu ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel