'Yan Majalisar Wakilai Sun Gayyaci Ministan Buhari Yazo Ya Musu Cikakken Bayani

'Yan Majalisar Wakilai Sun Gayyaci Ministan Buhari Yazo Ya Musu Cikakken Bayani

- Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana a gabanta don ya mata bayanin tsaron da filayen jirgin sama ke dashi.

- Majalisar tace ankai hare hare a filayen jirgin sama a Kaduna har an sace mutane 11

- A cewar Majalisar hakan wata babbar barazana ce ga harkokin sufirin jiegin sama a ƙasar nan.

Majalisar wakilai ta gayyaci ministan sufurin sama, Hadi Sirika, ya bayyana a gaban kwamitin jiragen sama domin yin bayani kan yadda yan bindiga suka shiga filin jiragen sama na Kaduna har suka dauke mutane 11.

A zaman ta ranar Laraba, majalisar ta amince da kudirin da Mr Musa Pali, ya kawo inda ya bukaci majalisa data gayyaci ministan sufurin jiragen sama.

Ministan, ya bayyana a gabanta ya mata bayani kan yadda akayi yan bindiga suka shiga filin jiragen sama na Kaduna da kuma yadda za'a kare afkuwar faruwar hakan nan gaba a filayen jiragen samar kasar nan.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Danbarwa ta ɓarke a majalisar dattijai kan Kudirin samar da Hukumar kula da Jami'an tsaro

Bayan yan majalisar sun amince da kudirin sun bukaci da shugaban 'yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, da sauran jamian tsaro a filayen jirage kasar nan da su kara tsaurara matakan tsaro.

Domin kiyaye kutse da kuma tabbatar da amso wadanda aka sace haɗe da kama masu laifin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kudirin mai taken 'bukatar kare filayen jiragen sama a fadin kasa'

Pali yace "Majalisa ta lura cewa a ranar 6 ga watan Maris 2021, yan bindiga sun mamaye wajen kwanan ma'aikatan hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya a Kaduna inda suka dauke mutane 11"

'Yan Majalisar Wakilai Sun Gayyaci Ministan Buhari Yazo Ya Musu Cikakken Bayani
'Yan Majalisar Wakilai Sun Gayyaci Ministan Buhari Yazo Ya Musu Cikakken Bayani @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa ta damu cewa idan hare-hare da sauran matsalolin tsaro suna faruwa a filayen kasar nan wadanda sune hanyoyi tafiya mafi aminci kuma wajen samun kudin shiga ga gwamnati to tafiya ta jirgin sama zata zama abin tsoro.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: An Ceto Mutane 10 Da Aka Sace daga Gidajen Ma'aikatan Filin Jirgin Sama a Kaduna

"Idan haka ta cigaba da faruwa zirga-zirgar sama a Najeriya zata fuskanci kalubalen," inji ɗan majalisar.

Ya ƙara da cewa: “Majalisa ta damu kan yadda rahoto ya nuna yan bindigan sun shiga gidajen kwanan ma'aikata har suka tafi da wasu mutane ciki harda ma'aikacin hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya"

Majalisa ta damu kan cewa idan ba'a inganta tsaron filayen jiragen Najeriya, hakan zai tsorata masu son zuwa Najeriya daga kasashen waje, waɗan da suka haɗa da masu zuba jari kuma hakan ka iya jawo hukunci daga hukumomi masu kula da harkar na kasashen duniya" Inji shi.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka gungun 'yan Boko Haram a Borno.

A wani samame da sojojin suka kai, sun kashe tare da kwato wasu kayayyaki a hannun 'yan ta'addan.

Daga cikin abinda aka kwato, an samu motoci da bindigogi kirar AK-47 da sauran makamai.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Online view pixel