Boko Haram: Mun gaji haka; Sojoji sun roki sabon Hafsun Soji ya basu dama su ga iyalansu
- Wasu Sojoji su na kukan cewa an bar su sun dade su na yaki da ‘yan ta’adda
- An yi sama da shekara biyar ba a sauya rundunar da ke fada a fagen fama ba
- Dakarun Najeriya sun nemi a ba su damar su je su gana da iyali da ‘yanuwa
Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya ya yi alkawari za a rika sauya dakarun da ke fiin daga, amma HumAngle ta ce har yanzu ba ayi wani abu a kai ba.
Jaridar ta ce wasu sojojin kasan sun shafe fiye da shekaru biyar su na yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram, wanda hakan ya sa duk karfinsu ya yi kasa a yanzu.
Sojojin da ke yaki da yankin Gamborun Ngala da Rann sun koka da cewa dade wa da su ka yi a filin daga ya sa sun gaji, su na bukatar wasu sojoji su canje su.
Ko a karshen watan Disamban shekarar da ta wuce, wasu sojoji sun gabatar da irin wannan korafi.
KU KARANTA: Kotu ta yi na’am da rokon EFCC na karbe gidajen Janar Mohammed
Da aka yi hira da wani soja da bai bari a bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa su na neman shiga shekara ta shida a wajen yaki, ba tare da sun ga iyalansu ba.
Ya ce: “Mun haura shekara biyar kenan yanzu a nan. Kwanakin baya wasu Musulmai daga cikin abokan aikinmu su ke kukan wannan ne azumi na biyar a nan.”
Sojan ya ce: “Kuma abin duk ya na yi mana wahala. Lamarin ya baci. Babu izza da karfin yaki.”
“Wannan abu da ake yi ya na karya karfin gwiwarmu, saboda yanzu hankalinmu ba a wajen yakin Boko Haram yake ba. Kukan da kowane soja yake yi kenan.”
KU KARANTA: Operation Thunder Strike sun hallaka wasu 'yan bindiga a Kaduna
Sojan kasan ya cigaba: “Wannan ne ya sa mu ke kira ga shugaban hafsun sojojin kasa ya yi wani abu a game da lamarin ta yadda za mu koma, mu ga ‘yanuwanmu.”
"Idan ya so, daga baya sai mu dawo mu canji wadanda su ke maye guraben na mu. A haka har za a samu karfin da za a tunkari makiya, a gama da Boko Haram.”
A jiya kun ji yadda mahukuntan gidan soja su ka yi wa sojoji afuwa na laifin gudu da su ka yi bayan an yi artabu da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno.
Da abokan gaba su ka taso sojoji a gaba, ana zargin rundunar Marte ta tsere daga filin daga
Hukumomin bataliya ta bakwai ta gidan sojojin kasa, ta yarda ta dawo da sojojin bataliya ta 153 da ke garin Marte, jihar Borno bayan abin da ya faru a kwanakin baya.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng