Rikici ya barke a majalisar dattawan Najeriya kan batun matsalar tsaro

Rikici ya barke a majalisar dattawan Najeriya kan batun matsalar tsaro

- Majalisar dattawan Najeriya ta kaure da rikici da hayaniya bayan gabatar da wani kuduri

- An gabatar da kudiri kan kafa hukumar da zata ke kula da harkokin tsaro a kasar Najeriya

- Kowa ya gagara sauraran dan uwansa, lamarin da ya jawo fadi in fadi a zauren majalisar

Wani rikici ta barke a majalisar dattawan Najeriya lokacin da 'yan majalisar ke tabka muhawara a kan wani kudurin da aka gabatar musu na bukatar a kafa hukumar da za ta kula da harkokin tsaron kasar, BBC Hausa ta ruwaito.

Wasu dai sun yi zargin cewa kudirin na nema ya kwace wa shugaban kasar ne ikonsa na nada hafsoshin tsaro.

KU KARANTA: Ba sace ni aka yi ba, na gujewa auren dole ne, amaryar da ake zargin an sace a Kano

Rikici ya barke tsakanin dattawan Najeriya kan batun matsalar tsaro
Rikici ya barke tsakanin dattawan Najeriya kan batun matsalar tsaro Hoto: Quartz
Asali: UGC

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Eyinnaya Abaribe ne ya gabatar da kudurin dokar, wanda wasu takwarorinsa daga bangarorin arewaci da kundancin kasar suka goya masa baya.

Kuma kudirin dokar na neman a kafa wata hukuma ce da za ta kula da harkokin tsaro, wato mai kula da harkokin sojojin kasa da na sama da kuma na ruwa.

Sai dai yana gabatar da kudurin hayaniya ta kaure a majalisar, inda masu goyon baya na yi masu suka da caccaka, ba mai sauraron dan uwansa.

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka gabatar da irin wannan kuduri a zauren majalisar dattawan, saboda a watan Maris din bara ma an gabatar da mai kama da shi amma bai kai labari ba.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka gungun 'yan Boko Haram a Borno

A wani labarin daban, Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya da ta dauki hayar sojojin kasashen waje domin yakar masu tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne sakamakon wani kudiri da Abdulkadir Rahis ya gabatar a ranar Laraba.

Kudirin na Mista Rahis ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake tsara dabarun yaki da masu tayar da kayar baya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel