Ba sace ni aka yi ba, na gujewa auren dole ne, amaryar da ake zargin an sace a Kano

Ba sace ni aka yi ba, na gujewa auren dole ne, amaryar da ake zargin an sace a Kano

- Wata amarya da ake zaargin masu garkuwa da mutane sun sace, ta bayyana gaskiyar lamarin

'- Ta bayyana karara cewa, ita ta shirya dukkan shirin da ya jawo aka zargi an sace ta ne

- Ta bayyana cewa, bata son mijin da za ta aura ne ya jawo ta gudu ta kuma shirye kamar an sace ta

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta ce ba a yi garkuwa da amaryar da za a aurar ba, Amina Gwani Danzarga tun da farko kamar yadda iyayenta da jama'a suka yi imani.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa Daily Trust cewa budurwar ta buya ne saboda ba ta son auren.

Ya ce budurwar ta shirya duk yadda aka yi tunanin ta bace, hakan ya sa iyayenta da mai neman ta suka yi imanin cewa an sace ta 'yan sa'o'i kadan zuwa shirin daurin auren nata.

Kiyawa ya kara da cewa tsawon kwanakin da yarinyar ta kwashe a boye, ta je wurare da dama don cimma burinta.

"Ana ci gaba da bincike domin gano duk wuraren da ta fake da kuma kiran wayar da ta yi a tsawon kwanaki hudu da ta yi tana boye," in ji shi.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka gungun 'yan Boko Haram a Borno

Ba sace ni aka yi ba, na gujewa auren dole ne, amaryar da ake zargin an sace a Kano
Ba sace ni aka yi ba, na gujewa auren dole ne, amaryar da ake zargin an sace a Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce, a matsayin wani bangare na dokar ‘yan sanda don kare rayukan mutane, rundunar ta dauki yarinyar zuwa asibiti don duba lafiyarta.

'Dalilin da ya sa na yi karyar sace ni'

Amina, a nata bangaren, ta ce ta shirya bacewar ta ne saboda ba ta kaunar mijin da za ta kasance.

"Tabbas, duk da cewa ni ne na gabatar da shi ga mahaifana daga baya ba na son saurayin shi ya sa na yanke wannan shawarin," in ji ta.

Amina ta kara da cewa, kamar yadda ta ke girmama iyayenta sosai, ba za ta iya sanar da su kwatsam ta sauya tunaninta game da mai neman nata ba.

Ta ce, amma yanzu tana son saurayin da kuma a shirye take ta zauna da shi cikin lumana har tsawon rayuwarta.

Ta kuma nemi afuwar iyayenta da saurayin da za ta aura, tana mai bayyana cewa cewa sharrin shaidan ne.

Kawun Amina, Gwani Rayyanuna Gwani Danzarga, ya nuna kaduwa game da lamarin.

“Har yanzu ina cikin kaduwa da abin da yarinyar ta aikata.

“Ita ce ta gabatar mana da shi kuma na yi bincike game da saurayin a matsayinmu na iyaye, mun yi dukkan tsare-tsaren da suka dace game da auren."

KU KARANTA: PDP: Gwamnatin APC yaudarar 'yan Najeriya kawai take, ba wani aiki da take samarwa

A wani labarin daban, Aisha Yesufu ta shawarci iyaye da ke tura 'ya'yansu makarantu a jihohin arewacin Najeriya dake fuskantar matsalar tsaro da su hakura su killace yaran na wani lokaci kafin gwamnati ta samar da mafita mai dorewa.

Biyo bayan sace dalibai da aka yi na baya-bayan nan a jihar Kaduna, 'yan Najeriya na ci gaba da nuna juyayi da Allah-wadai da kai hare-haren 'yan bindiga a fadin arewacin Najeriya.

Masu fada aji a kasar, na bayyana ra'ayoyi da shawarwarinsu ga gwamnati hade da iyaye kan matakan da ya kamata a dauka domin magance matsalar da ta dumfaro arewacin Najeriya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel