Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya

Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya

- Fitacciyar mawakiya kuma 'yar kasuwa Rihanna ta siya wani katafaren gida mai bada sha'awa

- Rihanna ta siya gidan a kan kudi $13.8 miliyan kuma yana nan a Beverly Hill kusa da gidan Madonna

- Gidan yana kunshe da dakunan bacci biyar, bandakuna 7, wurin wanka, gyaran jiki da tsibirai biyu

Mawakiya kuma 'yar kasuwa Rihanna ta siya wani katafaren tangamenen gida a Beverly Hills mai darajar dala miliyan 13.8.

Gidan mai dakunan bacci biyar, yana da bandakuna bakwai kuma an gina shi ne a wani tsauni mai girman kafa 21,958 kamar yadda The Dirt ta tabbatar.

Makwabtanta da gidajensu ke kusa da juna sun hada da Madonna da Mariah Carey, wadanda suka siya gidajensu kusa da juna a shekaru masu yawa da suka gabata.

An gina gidan tun farko a shekarar 1938 kuma Mary Sheldon ce ta fara mallakarsa.

Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya
Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hare-haren 'yan bindiga: Ba za mu garkame makarantun jihar Kaduna ba, El-Rufai

Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya
Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Cikin gidan ya kunshi fili kato, wurin wanka, wurin gyaran jiki da sauransu. Akwai dakin girki, tsibirai biyu da sauran ababen more rayuwa.

Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya
Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Ta siya gidan ne bayan mako daya da aka dinga bada labarin za ta fadada kasuwancinta na kayan gyaran jiki inda zata hada da kayan gyaran gashi da zata saka mishi suna Fenty Hair.

Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya
Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya
Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock

A wani labari na daban, mayakan Boko Haram dauke da makamai sun shiga kauyen Katarko dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe inda suka kone wata makarantar firamare da dakin shan magani.

Lamarin ya faru da karfe 5:30 na safiyar Talata yayin da Musulmai ke sallar Asubahi. Katarko gari ne mai nisan kilomita 18 daga Damaturu wanda ke fuskantar hare-hare masu tarin yawa har da tashin bam a wata gada da ta hada Katarko da Buni Yadi da Biu a baya.

Vanguard ta ruwaito cewa, wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Ahmed ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun fatattaki sojoji wanda hakan yasa jama'a suka dinga neman wurin tsira.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel