Masari: Abin Da Ya Sa Ƴan Bindiga Suka Fi Son Nigeria Fiye da Mali

Masari: Abin Da Ya Sa Ƴan Bindiga Suka Fi Son Nigeria Fiye da Mali

- Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya ce arzikin da Nigeria ke da shi yasa yan bindiga ke addabar kasar

- Masari ya bada misalin cewa a wasu kasashen yankin Sahel masu garkuwa ba su samun kudi kamar yadda suke samu a Nigeria

- Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso Yamman, ya ce lamarin tsaro ta inganta tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce akwai arziki a Nigeria hakan yasa masu garkuwa ke addabar kasar, rahoton Daily Trust.

A yayin da ake zantawa da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Laraba, Masari ya ce masu garkuwa sun addabi Nigeria ne saboda albarkatun da ke kasar.

Masari: Abin Da Ya Sa Yan Bindiga Suka Fi Son Nigeria Fiye da Mali
Masari: Abin Da Ya Sa Yan Bindiga Suka Fi Son Nigeria Fiye da Mali. Hoto: @daily_trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma ya jaddada cewa arzikin da ke Nigeria ne yasa masu garkuwa ke kwararowa kasar daga yankin Sahel ta nahiyar Afirka.

Kasashen da ke yankin Sahel sun hada da Senegal, Mauritania, Mali, Burkina Faso, Algeria, Niger, Nigeria, Chad, Sudan da Eritrea.

Ya kuma yi ikirarin cewa an samu cigaba a bangaren tsaro tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki idan aka kwatanta da 2015 a lokacin da mutane ke fargabar zuwa masallatai da coci.

KU KARANTA: An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

"Haka lamarin ya ke a yanzu? Ba daya bane. Eh, akwai yan bindiga amma ka duba matsayin Nigeria a yankin Sahel ta Nigeria. Ba mune mafi arziki ba? Don haka, wannan dalili ne da zai janyo hankalin masu garkuwa su zo Nigeria. Idan ka sace mutum a Mali, ina za ka samu dubban kudi? Idan ka sace mutum a Nigera, za ka samu miliyoyi. Don haka dukkan mu sai mun tashi tsaye," wani sashi cikin jawabin Masari.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel