Dawisu ya yi kaura daga Najeriya inda ya koma kasar waje da zama

Dawisu ya yi kaura daga Najeriya inda ya koma kasar waje da zama

- Dakataccen hadimin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya yi kaura daga kasarsa ta haihuwa

- Yakasai ya bar Najeriya zuwa wata kasa da ba a tabbatar da ko ina bane

- Tsohon hadimin na Ganduje ne ya wallafa labarin barinsa kasar a shafinsa na Twitter tare da yin hamdala kan haka

Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimakawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano kan harkokin yada labarai, ya koma kasar waje.

Ganduje ya kori Yakasai a watan Fabrairu bayan ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan karuwar rashin tsaro.

KU KARANTA KUMA: 2023: Matasa 5,000 sun nemi PDP ta sanya Wike a takarar zaben Shugaban kasa

Dawisu ya yi kaura daga Najeriya inda ya koma wata kasar da zama
Dawisu ya yi kaura daga Najeriya inda ya koma wata kasar da zama Hoto: @dawisu
Source: Twitter

Daga nan ne kuma sai jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka damke Yakasai wanda aka tsare na tsawon kwanaki.

A wasu hotuna da ya saka a shafin sada zumunta, an ga Yakasai a filin jirgin saman wata kasar da ba a san ko waccece ba.

An kuma ga jirgin saman kasar Qatar a bayan hoton. Ya rubuta a shafinsa na Twitter "Sai wata rana Naija! Alhamdulillah!"

KU KARANTA KUMA: An samu rudani a Kaduna yayinda El-Rufai da ma’aikata suka ba da umarni daban-daban kan rufe makarantu

Ga yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a kasa:

A wani labarin, Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar nan da wa'adin da yake basu tare da jan kunne.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam'iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

A ranar Juma'a ne jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kutsa kwalejin harkar noma da gandun dabbobi dake Kaduna suka kwashe dalibai.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit

Online view pixel