FEC ta amince da aikin gyaran matatar man fetur dake Patakwal kan $1.5 biliyan
- Majalisar zartarwar kasar nan ta amince da aikin gyaran babbar matatar man fetur dake Patakwal kan kuɗi $1.5 Biliyan.
- Ministan albarkatun man fetur ne ya bayyana haka bayan fitowa daga taron majalisar na sati-sati a yau Laraba.
- Yakuma bayyana cewa za'a gudanar da aikin ne a mataki uku, kuma kamfanin kasar italiya aka bawa aikin
Majalisar zartawa ta ƙasar nan ta amince da fidda kuɗaɗe kimanin $1.5 biliyan don gyara babbar ma'aikatar ta ce man fetur dake Patakwal, babban birnin jihar Rivers, The Nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: 'Yan sanda sun cafke matashin da ya lakadawa dattijo duka a Kano, ya sheka lahira
Ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana haka ga manema labarai dake gidan gwamnati bayan taron majalisar zartawar na sati-sati, wanda shugaban Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Ministan ya ƙara da cewa, za'ai aikin gyaran ne a mataki uku, watanni 18, watanni 24, da kuma watanni 44, ya kuma bayyana cewa kamfanin italiya aka baiwa aikin, wanda kwararru ne a fannin.
Ministan yace:
"Ma'aikatar albarkatun man fetur ta gabatar da daftarin gyaran matatar mai dake Patakwal a taron majalisar zartarwa, kuma ta gabatar da kuɗin da aikin zaici $1.5 biliyan, kuma an amince da hakan nan take."
KARANTA ANAN: 2023: Matasa 5,000 sun nemi PDP ta sanya Wike a takarar zaben Shugaban kasa
"Saboda haka muna farin cikin sanar daku za'a fara aikin gyaran matatar man letur ɗin a mataki uku, matakin farko za'a kammala shi cikin watanni 18, wanda shine zai ba ma'aikatar damar samar da 90% na abinda ake tsammanin zata iya," a cewar ministan.
"Sannan za'a kammala mataki na biyu a cikin watanni 24, sai kuma matakin karshe da ake sa ran kammala shi cikin watanni 44." inji shi.
Daga ƙarshe ministan yace wannan labari ne mai daɗi ga 'yan Najeriya.
A wani labarin kuma Tsohon Gwamna Fayose ya je Minna, ya tuntubi Janar Abdulsalami da IBB a kan siyasar 2023
Ayodele Peter Fayose ya zauna ne da tsofaffin sojojin da su ka mulki Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar.
Kamar yadd a ya bayyana a shafinsa na Twitter, Fayose ya kai wa dattawan wan nan ziyara ne a farkon makon nan, ranar 15 ga watan Maris, 2021.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng