Tsohon Gwamna Fayose ya je Minna, ya tuntubi Janar Abdulsalami da IBB a kan siyasar 2023

Tsohon Gwamna Fayose ya je Minna, ya tuntubi Janar Abdulsalami da IBB a kan siyasar 2023

- Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya tattara ya kai ziyara zuwa Minna

- Fayose ya yi zama da Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar

- Ana tunanin wannan zama ba ta rasa dangataka da shirin takarar Fayose a 2023

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya kai ziyara zuwa garin Minna, jihar Neja, ya gana da tsofaffin shugabannin kasar nan.

Ayodele Peter Fayose ya zauna ne da tsofaffin sojojin da su ka mulki Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, Fayose ya kai wa dattawan ziyara ne a farkon makon nan, ranar 15 ga watan Maris, 2021.

The Nation ta ce ziyarar da Ayo Fayose ya kai wa tsofaffin shugabannin, ba za ta rasa nasaba da burinsa na fito wa takarar shugaban kasa ba.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta samu karin 'Dan Majalisar Wakilai

Mista Fayose ya na cikin ‘yan siyasar da su ke harin kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Da yake bada labarin zamansa da tsofaffin shugabannin sojoji a shafinsa na @AyoFayose, tsohon gwamnan ya ce ya na cigaba da ‘tuntubar manya’.

A cewar Ayodele Fayose, tattaunawar sa da Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar ta shafi harkar tattalin arziki, siyasa da harkar tsaro ne.

“Yau a garin Minna, jihar Nija, na hadu da tsofaffin shugabannin kasa biyu; Janar Ibrahim Badamasi Babangida and Janar Abdulsalami Abubakar.”

KU KARANTA: Lokaci ya yi: Shugaban ICRC ya rasu

Tsohon Gwamna Fayose ya je Minna, ya tuntubi Janar Abdulsalami da IBB a kan siyasar 2023
Janar Abdulsalami Abubakat da Ayo Fayose Hoto; GovAyoFayose
Asali: Twitter

“Mun yi tattauna wa mai riba a game da yadda za ceto sha’anin tsaron kasar nan, da matsalolin tattalin arziki da kuma kalubalen siyasa.” Inji Fayose.

Babban jagoran jam’iyyar adawar a Kudu maso yamma ya nuna har yanzu bai tsaida matsaya a kan takara a 2023 ba, ya ce ya na cigaba da tuntube-tuntube.

A lokacin da hankali ya karkata zuwa 2023, mun kawo maku jerin Ministocin Tarayya masu-ci da ake tunanin su na harin takarar Gwamna a asalin jihohinsu.

Masu fashin-baki da nazarin siyasar gida su na ganin irinsu Hadi Sirika, Abubakar Malami, da Saleh Mamman su na da shirin neman takarar gwamnoni.

Manyan kusoshin Gwamnatin na APC ka iya zuwa gida su yi takarar Gwamnonin jihohi a 2023.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng