'Yan sanda sun cafke matashin da ya lakadawa dattijo duka a Kano, ya sheka lahira

'Yan sanda sun cafke matashin da ya lakadawa dattijo duka a Kano, ya sheka lahira

- 'Yan sandan jihar Kano sun damke matashin da ya lakadawa mahaifin abokinsa duka

- Sakamakon yi wa dattijon mai shekaru 60 dukan tsiya, likitoci sun tabbatar da rasuwarsa

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Haruna Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta damke wani matashi da yayi sanadin mutuwar wani dattijo mai shekaru 60 kuma mahaifin abokinsa bayan ya lakada masa mugun duka.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin a yammacin Talata.

Lamarin ya faru ne a unguwar sheka dake birnin Kano sakamakon takaddamar da ta hada matashin da mahaifin abokinsa.

KU KARANTA: Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024

'Yan sanda sun cafke matashin da ya lakadawa dattijo duka a Kano, ya sheka lahira
'Yan sanda sun cafke matashin da ya lakadawa dattijo duka a Kano, ya sheka lahira. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

A cewar Kiyawa, samun bayanin aukuwar lamarin ce tasa suka garzaya wurin kuma likitoci ne suka tabbatar da mutuwar dattijon.

Dattijon mai suna sale Usman yana zaune a wurin sana'arsa yayin da matashin ya sheke shi.

Duk da dai dan marigayin yace babu wata rashin jituwa tsakaninsu, don haka bai san dalilin matashin na yin haka.

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane

A wani labari na daban, rundunar 'yan sanda a ranar Talata ta damke wata kungiyar masu laifi 9 dake siyar da bindigogi kala-kala ga 'yan bindigan daji, masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauransu.

Daga cikin wadanda ake zargin kuma aka kama, akwai wani mai suna Anthony Base, wanda aka kama, aka gurfanar sannan aka kai shi gidan yari saboda wannan laifin amma sai wani gwamnan arewa maso yamma yayi masa rangwame aka sako shi.

A yayin da aka kai wadanda ake zargin tsohuwar hedkwatar sashi na musamman dake yaki da fashi da makami a Abuja, kakakin rundunar, Frank Mba, ya koka da yadda makamai da miyagun kwayoyi ke yawo a kasar nan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: