Yanzu-Yanzu: An Ceto Mutane 10 Da Aka Sace daga Gidajen Ma'aikatan Filin Jirgin Sama a Kaduna

Yanzu-Yanzu: An Ceto Mutane 10 Da Aka Sace daga Gidajen Ma'aikatan Filin Jirgin Sama a Kaduna

- Sojoji sun yi nasarar ceto mutane 10 da yan bindiga suka sace daga gidajen ma'aikatan filin jiragen sama

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan

- Samuel Aruwan ya ce gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi farin cikin samun labarin ceto mutanen ya kuma yi musu fatan alheri

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa sojoji sun ceto mutane 10 da aka sace daga rukunin gidajen ma'aikatan filin jiragen sama da ke Ifira, karamar hukumar Igabi.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

DUBA WANNAN: An Rasa Rayuka Sakamakon Hatsarin Da Trela Dauke da 'Yan kasuwa 70 Ta Yi a Bauchi

Yanzu-Yanzu: An Ceto Mutane 10 Da Aka Sace daga Gidajen Ma'aikatan Filin Jirgin Sama a Kaduna
Yanzu-Yanzu: An Ceto Mutane 10 Da Aka Sace daga Gidajen Ma'aikatan Filin Jirgin Sama a Kaduna. Hoto: Samuel Aruwan
Source: Facebook

Ya bada sunayen wadanda aka ceto kamar haka: Mr. Ilori Sunday, Mrs. Celestina Sunday, Miss Beauty Oshaibie Sunday, Miss Miracle Sunday, Miss Marvelous Sunday, Miss Destiny Sunday, Mr. Samuel Sunday, Miss Deborah Sunday, Hajiya Badiyatu Abdullahi Gambo da Bilkisu Gambo.

Idan za a iya tunawa yan bindiga dauke da makamai sun haura katangar rukunin gidajen ma'aikatan filin jirgin saman a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Maris inda suka sace mutane 10 a gidajen da ke kusa da katanga.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban JAMB Kan Almundahar N900m

A cewar kwamishinan, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi farin cikin samun rahoton ceto su inda ya taya rundunar sojojin murnar samun nasara.

Ya kuma gana da mutanen da aka ceto inda ya karfafa musu gwiwa sannan ya basu tabbacin cewa gwamnatin Kaduna za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa don tsare lafiyar su.

"Ya yi musu fatan alheri a yayin da aka sada su da iyalansu da masoyansu," ya kara da cewa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Online view pixel