Ministocin Buhari 6 da za su iya ajiye mukamansu, su tafi takarar Gwamna a 2023

Ministocin Buhari 6 da za su iya ajiye mukamansu, su tafi takarar Gwamna a 2023

Akwai wasu Ministocin gwamnatin tarayya da masu fashin-baki da nazarin siyasar gida su ke ganin cewa su na da shirin neman takarar gwamna.

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin wadannan Ministoci na gwamnatin Muhammadu Buhari da za su nemi su koma gida a zabe mai zuwa.

1. Timipre Sylva

Har yanzu Timipre Sylva ya na ragowar wa’adi daya a gidan gwamnatin Bayelsa, shiyasa ake ganin zai sake neman takara, amma siyasar 2020 ta nuna kamar Ministan ya hakura da kujerar.

2. Mustapha Baba Shehuri

Hon. Mustapha Baba Shehuri ya na sha’awar kujerar gwamna, wannan ya sa ya nemi tikitin APC a jihar Borno a 2018, Ministan zai fuskanci kalubale a 2023 daga wurin gwamna Babagana Zulum

KU KARANTA: Yaudarar jama'a Gwamnatin Buhari ta ke yi - PDP.

3. Hadi Sirika

Hadi Sirika fitaccen ‘dan siyasar Katsina ne wanda ya rike kujerar majalisar wakilai da ta dattawa, ana ganin ya na cikin masu burin gadar Aminu Bello Masari a gidan gwamnati.

4. Abubakar Malami

Akwai yiwuwar cewa Abubakar Malami SAN zai nemi takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin APC a 2023. Babban lauyan gwamnatin tarayya ya na cikin manyan kusoshin jam’iyyar APC.

5. Gbemisola Saraki

Wasu na ganin cewa har gobe Karamar Ministar sufuri ta kasa, tsohon burin Ruqayyat Gbemisola Saraki, na zama gwamnan Kwara ya na nan. Yanzu haka ba ta ga maciji da gwamna mai-ci.

KU KARANTA: PDP za ta fitar da matsaya game da takarar 2023

Ministocin Buhari 6 da za su iya ajiye mukamansu, su tafi takarar Gwamna a 2023
Wasu Ministoci Hoto: legit.ng
Source: UGC

6. Saleh Mamman

A halin yanzu har wasu magoya-baya sun fara fito da fastocin Taraba 2023 sai Saleh Mamman. Ana kyautata zaton Ministan wutan ya na kwadayin kujerar gwamnan jihar Taraba a APC.

A makon nan kun samu labari cewa jam'iyyar hamayya ta PDP ta budawa Dr. Goodluck Jonathan hanya yayin da aka nemi a fito da 'dan takarar shugaban kasa zuwa Kudu maso Kudu a 2023.

Wani jigon PDP na jihar Edo, ya ce ba a kyauta masu a 2015 da aka hana Jonathan tazarce a ofis ba.

Shugaban PDP na Edo, Mista Tony Aziegbemi, ya na cewa ya kamata mutumin Kudu maso kudu ya samu tikiti a 2023. domin a shafe bukulun da aka yi wa yankin Neja-Delta a zaben 2015.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel