Ba zamu dakatar da rigakafin COVID19 ba, Inji hukumar NAFDAC

Ba zamu dakatar da rigakafin COVID19 ba, Inji hukumar NAFDAC

- Hukumar kula da ingancin abinci da kuma kwayoyi ta kasa tace mutane na mutuwa da korona saboda haka baza'a dakatar da rigakafin ba

- Shugabar Hukumar NAFDAC ce ta fadi haka a wata fira da tayi da gidan talabishin na Channels TV

- Tace ta yi imani cewa amfanin da rigakafin Astrazeneca ke da shi ya zarta illar ta saboda haka be kamata a dakatar da yin rigakafin ba

Hukumar kula da ingancin abinci da ƙwayoyi ta ƙasa (NAFDAC) ta ƙara jaddada maganarta na cewa bai kamata a dakatar da allurar rigakafin korona ta Astrazeneca a Najeria ba, duk da tsoron da ake yi na allurar na da illa a ɓangare ɗaya.

KARANTA ANAN: Tambuwal Ya Musanta Jita-Jitar Cewa Anyi Ƙoƙarin Sace Ɗalibai A Sokoto

Shugabar NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta faɗi haka ne a wata zantawa da ta yi da kafar yaɗa labarai Channels TV a shirin 'Sunrise Daily.'

Mojisola Adeyeye, ta ƙara da cewa: "Mutane na mutuwa da COVID19, kuma na yi imani kodan mutuwar da mutane ke yi bai kamata a dakatar da allurar rigakafin ba."

"Bai kamata a dakatar da allurar ba matuƙar ba illarta ce tayi yawa ba," a cewarta.

Mutane na mutuwa, Bazamu dakatar da rigakafin COVID19 ba, Inji NAFDAC
Mutane na mutuwa, Bazamu dakatar da rigakafin COVID19 ba, Inji NAFDAC Hoto: @NafdacAgency
Asali: Twitter

Duk da cewa ƙasashe a sassa daban-daban na duniya sun dakatar da yin rigakafin saboda abinda ka iya zuwa ya dawo kamar cutar jini, shugaban tace ta na da yaƙinin amfanin rigakafin yafi illarta yawa.

KARANTA ANAN: Rikicin Hijabi: Kiristoci sun rufe kofofin shiga makaranta yayinda gwamnati ta bada umurnin budesu

"Mun sani cewa abubuwan dake faruwa game da allurar rigakafin abin a duba ne, amma kuma amfaninta yafi illar yawa," shugabar ta faɗa.

Shugabar NAFDAC ɗin ta bayyana cewa akwai bukatar jin ta bakin mutane don sanin yadda suka ɗauki rigakafin a yanzu.

Tace "Rigakafin ba ita ce ta farko da aka amince da ita cikin gaggawa ba, rigakafin COVID19 na taimakawa sosai ga waɗanda akayi mawa ita."

A wani labarin kuma Rundunar sojin Nigeria ta ragargaji mayakan Boko Haram a wani arangama.

Sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a harin da suke kai wa 'yan ta'addan Boko Haram, ISWAP da sauran su.

Dakarun Bataliya ta 81 tare da hadin gwiwar' yan kato da gora a yammacin ranar Litinin, 15 ga Maris, sun kashe karin 'yan ta'addan a yankin Dikwa, Jihar Borno.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262