2023: Jigon PDP a Edo ya na yi wa tsohon Shugaba Jonathan kokarin komawa Aso Villa

2023: Jigon PDP a Edo ya na yi wa tsohon Shugaba Jonathan kokarin komawa Aso Villa

- Shugaban PDP na jihar Edo ya na goyon bayan Kudu maso kudu ya sake takara

- Tony Aziegbemi ya na kiran PDP ta ba yankin na su tikitin shugaban kasa a 2023

- Jigon jam’iyyar ya ce ba a kyauta masu da aka hana Jonathan tazarce a 2015 ba

Bangaren jam’iyyar PDP ta jihar Edo, ta ba uwar-jam’iyya shawara ta kai takarar shugaban kasa a zaben 2023 zuwa shiyyar Kudu maso kudu.

Jaridar Punch ta rahoto shugaban PDP na Edo, Mista Tony Aziegbemi, ya na cewa ya kamata mutumin Kudu maso kudu ya samu tikiti a 2023.

Tony Aziegbemi ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2021, a lokacin da ya zanta da manema labarai a garin Benin, jihar Edo.

Jagoran jam’iyyar hammayar ya ce an yi masu bukuku a lokacin da aka hana Goodluck Jonathan damar zarce wa a kan kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA: Ba da mu ba; ‘Yan Neja-Delta sun ce ba su goyon bayan Biayafara

Aziegbemi ya ce jam’iyyar PDP ta na da jiga-jigan da za su ci mata zabe mai zuwa a yankinsu.

“Yayin da 2023 ta ke karaso wa, ina kira da cewa jam’iyyarmu ta na da dinbin mutanen da za ta iya kai ta ga nasara a duka bangarori shida na kasar nan.”

Ya ce: “Ina ganin cewa an yi wa yankinmu na Kudu maso kudu kafa a lokacin da aka hana shugaban kasa (Goodluck) Jonathan damar tazarce a ofis.”

“Saboda sanin wannan da kuma irin shugabannin da mu ke da su a yankin, mu na kira ga jam’iyyarmu ta PDP ta kai takara zuwa Kudu maso kudu.”

2023: Jigon PDP a Edo ya na yi wa tsohon Shugaba Jonathan kokarin komawa Aso Villa
Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus
Asali: UGC

KU KARANTA: Kungiyar Gwamnoni za ta yi zama na musamman a gobe

A cewar Tony Aziegbemi, idan aka yi haka, an shafe zaluncin da aka yi wa yankin a 2015.

Kwanaki sai da jam'iyyar APC mai mulki ta fito ta karyata rahotannin cewa tana zawarcin Goodluck Jonathan domin ya yi mata takara a zaben 2023.

Shugaban riko na jam'iyyar ta APC, Gwamna Mai Mala Buni ya ce wasu masu wata muguwar manufar siyasa ne suka kirkiri wannan jabun labari a kasar.

Haka zalika wani tsohon hadimin tsohon shugaban kasar ya karyata rade-radin takarar shugaban kasa da komawar Goodluck Jonathan jam'iyyar APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng