Kasashen nahiyar Afrika 10 masu kudi mafi daraja a 2021
Mutane da dama sun san kudaden kasashen nahiyar Afrika amma ba kowa ya san darajar wadannan kudade ba idan aka kwatantasu da dalar Amurka.
Hakan ya sa Legit.ng ta kawo muku jerin kasashe 10 masu kudade mafi daraja a nahiyar Afrika.
Ga jerinsu:
1. Dinari na kasar Libya
Dinarin kasar Libya ne kudi mafi daraja a nahiyar Afrika (1 USD – 1.43 LYD).
2. Dinarin Tunisiya
Dinarin kasar Tunisiya ne kudi mafi daraja na biyu a nahiyar Afrika (1USD – 2.90 TND).
3. Cedi na kasar Ghana
Kudin Ghana, Cedi, ya farfado bayan aiki tukuru na gwamnatin da kasar tayi, yanzu shine mai daraja na uku a Afrika (1USD – 5.75 CEDI)
4. Dirham na kasar Maroko
Dirhamin kasar Maroko ne kudi mafi daraja na hudu a Afrika (1 USD – 9.87 Mad).
5. Pula na kasar Botswana
Kasar Botswana ce kasa ta biyar mafi kudi mai daraja a Afrika (1 USD – 11.86 Pula).
KU KARANTA: Hotunan cikin tankamemen katafaren gidan $13.8m da Rihanna ta siya
6. Nafka na kasar Eriteria
Nafka na kasar Eriteria ne kasa na shida a jerin kudaden masu daraja a Afrika (1 USD – 15.00 ERN).
7. Fam na kasar Masar
Fam na Kasar Masar ne kudi mafi daraja na bakwai a Afrika (1 USD – 15.75 EGP).
8. Kwacha na kasar Zambiya
Kasar Zambia ta shahara na arzikin ma'adanin Copper. Kudin kasar ce mafi daraja ta takwas a Afrika
DUBA NAN: NDDC ta fallasa Gwamnonin N/Delta 9, an ba kowace Jiha N100m a matsayin tallafin COVID-19
9. Rand na kasar Afrika ta kudu
Kasar Afrika ta kudu na da tattalin arziki mai karfi amma kudinta ne na bakwai cikin jerin masu karfi a nahiyar.
10. Fam na kasar Sudan
Duk da matsalolin da kasar Sudan ke fama da shi, kudinta na cikin jerin mafi karfi a Afirka
Asali: Legit.ng