Shugaban EFCC ya samu damar yin gwanjon dukiyoyi da kadarorin babban Soja

Shugaban EFCC ya samu damar yin gwanjon dukiyoyi da kadarorin babban Soja

- Kotu ta ba EFCC damar karbe gidaje da filayen Janar Jafaru Mohammed

- Wasu gidajen da Janar Jafaru Mohammed ya mallaka za su bar hannunsa

- Kotu ta ba sojan kwanaki 14 domin ya kare kansa, a hana karbe kadarorin

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta shiga kotu da wani jami’in soja, Birgediya Janar Jafaru Mohammed.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa EFCC ta fara yin nasara a kotu inda Alkali ta yi na’am da rokonta na karbe wasu daga cikin dukiyoyin sojan kasan.

Alkali mai shari’a, Folashade Ogunbanjo, ta amince wa hukumar EFCC da ta rike wasu gidaje takwas da Janar Jafaru Mohammed ya mallaka a Najeriya.

Kotu ta yi na’am da rokon da shugaban EFCC ya gabatar a ranar 9 ga watan Maris, 2021.

KU KARANTA: Mai laifin da aka yi wa afuwa ya cigaba da saida makamai

Folashade Ogunbanjo ta bukaci EFCC ta wallafa sunayen kadarorin wannan soja da aka karbe, a tallata su domin masu sha’awa su fito su nuna bukatarsu.

Alkalin ta bada tsawon makonni biyu domin Birgediya Janar Jafaru Mohammed ya kare kansa, ya gamsar da kotu a kan a hana karbe dukiyarsa har abada.

Gidajen sojan ko kuma na-kusa da shi da aka amince EFCC ta karbe sun hada da wani gida da ke unguwar gidajen God’s Own Estate a birnin tarayya, Abuja.

Sai wani gida a Jubril Aminu Crescent, Katampe, da fili a Kubwa Express, kusa da Abuja Model City Gate, da wani gida a Kabusa Garden Estate, duk a Abuja.

Shugaban EFCC ya samu damar yin gwanjon dukiyoyi da kadarorin babban Soja
Sabon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hukumomi sun yi wa Sojoji afuwa na laifin gudu daga filin yaki

Sauran gidajen wannan soja sun hada da: Gidaje masu lamba #15, #21 Crescent, 2nd Avenue, Gwarinpa Estate, da #3 Liverpool Close, Sun City Estate, Abuja.

Akwai wasu gidaje biyu a Mainstreet, Sun City Estate, Abuja; da kan layin Osaka Street, Sun City Estate, Abuja.

A yau Laraba, kun ji cewa Sanatocin kasar nan su na shirin binciken hannun Gwamnoni Neja-Delta a badakalar da NDDC ta tafka na batar da Naira biliyan 6.

Ma'ikatar NDDC da aka kafa domin kula da cigaban yankin Neja-Delta ta na ikirarin ta batar da Naira Biliyan 6.25 wajen bada tallafin Coronavirus a shekarar 2020.

Shugaban rikon NDDC ya ce har Gwamnoni sun samu kaso a kudin tallafin annobar cutar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel