Boko Haram: An dawo da Sojoji 145 da aka dakatar bayan sun sulale daga filin yaki

Boko Haram: An dawo da Sojoji 145 da aka dakatar bayan sun sulale daga filin yaki

- An dawo da sojojin kasa 145 da su ke garin Marte aiki bayan an dakatar da su

- Hukumomin gidan soja sun hukunta jami’an sojojin ne bayan an kai masu hari

- Kwanan baya ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai munanan hare-hare a Marte

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin bataliya ta bakwai ta gidan sojojin kasa, ta yarda ta dawo da sojojin bataliya ta 153 da ke garin Marte, jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ce an dawo da sojojin bakin-aiki ne bayana an karbe khakinsu da takardar aiki bayan ‘yan Boko Haram sun kai masu wasu hare-hare.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun samu galaba a kan jami’an sojojin kasar a wasu hare-hare da aka kai a cikin watannin Junairu da Fabrairun wannan shekarar.

KU KARANTA: Shugabar BBOG ta ce ana kokarin yin rufa-rufa kan kudin makamai

Duk da hujjojin da aka samu, hedikwatar tsaro ta musanya rahoton cewa an dakatar da wasu sojojin kasa bayan abin da ya auku da dakarun kasar a Marte.

Tsere wa daga filin yaki saboda tsoron gwabza wa da abokan gaba babban laifi ne a gidan soja.

Rahoton da aka fitar a ranar Laraba yake cewa: “Sojojin da abin ya shafa sun koma bakin aiki, an dawo masu da kayansu, an maida masu takardar shaidarsu.”

“Za su shiga cikin dakarun 212, 195 da 159, ya danganta da bataliyar da aka jefa sunayensu.”

KU KARANTA: Duk da hare-hare, ba za mu garkame makarantun Kaduna ba - El-Rufai

Boko Haram: An dawo da Sojoji 145 da aka dakatar bayan sun sulale daga filin yaki
Shugaban hafsun sojojin kasa, Attahiru Ibrahim
Asali: Getty Images

“Duk da cewa an maye gurabensu a Marte da wasu sojoji da aka dauko daga makarantar soji ta Jaji, jihar Kaduna, za su iya cigaba da zama a jihar Borno.”

Majiyar gidan sojan ta ce tun a 2017 aka tura wadannan sojoji zuwa Borno, sun shafe shekaru kusan hudu kenan ba tare da an dauke su daga filin daga ba.

An rahoto cewa munanan hare-haren Boko Haram sun yi sanadiyyar da wasu sojojin kasa fiye da 100 su ka arce daga filin yaki a yankunan Marte da kuma Dikwa.

Daga baya rundunar jami'an Sojoji dauke da jiragen yaki sun kawar da yan ta'addan ISWAP da suka kai hari a babban barikin sojoji dake Marte, jihar Borno.

Kakakin sojojin kasa, Janar Mohammed Yerima ya ce sojoji ba su arce daga filin daga ba

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel