Da duminsa: Jamhuriyar Nijar ta baiwa Buhari lambar yabo mafi daraja

Da duminsa: Jamhuriyar Nijar ta baiwa Buhari lambar yabo mafi daraja

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu jinjina daga gwamnatin jamhuriyar Nijar a ranar Talata, 16 ga Maris

- Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ne ya baiwa Buhari lambar yabon mafi daraja a kasar Nijar

- Ana kiran lambar yabon da Grand Croix Des Ordre National Du Niger kuma ana baiwa mutum mai nagarta da ya nuna gwarzantaka ne

Grand Croix Des Ordre National Du Niger, ita ce lambar yabo mafi daraja ta kasar Nijar kuma an baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 16 Maris, 2021.

Wannan karramawar na daga cikin abubuwan da suka faru yayin da shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya ziyarci shugaban kasa Buhari a fadarsa dake Abuja a ranar Talata.

KU KARANTA: FG tayi martani ga ikirarin Asari Dokubo na kafa sabuwar gwamnatin Biafra

Da duminsa: Jamhuriyar Nijar ta baiwa Buhari lambar yabo mafi daraja
Da duminsa: Jamhuriyar Nijar ta baiwa Buhari lambar yabo mafi daraja. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya sallami darakta janar na hukumar NiMet, yayi muhimman nade-nade 3

Buhari yace shugaban abun koyi ne tare da taya shi murnar kammala mulkinsa karo na biyu da kuma nasarar kyautar Mo Ibrahim da ya samu ta shugabancin Afrika.

Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina yace shugaba Buhari yace: "Ina taya jama'ar Nijar murna da zaben da suka yi cikin aminci tare da kwanciyar hankali.

"Nasarar da ka samu a lokacin mulkinka ta bayyana ne ta kyautar Mo Ibrahim da ka samu.Tabbas ka kara kima da daraja a gida da kuma kasashen dake makwabtaka daku da suka hada da Najeriya."

A wani labari na daban, mayakan ta'addanci na Boko Haram sun yi garkuwa da wasu makiyaya tare da yin awon gaba da shanunsu. Hakazalika, 'yan Boko Haram sun kashe makiyaya 22 a jihar Borno.

SaharaReporters ta tattaro cewa an kashe makiyayan ne a ranakun karshen makon da ya gabata a Monguno.

Mai bada shawara na musamman kan tsaron kasa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babagana Monguno daga Monguno yake.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng