Gwamnonin Jihohi 36 za su yi zama na musamman game da sha’anin farashin fetur

Gwamnonin Jihohi 36 za su yi zama na musamman game da sha’anin farashin fetur

- Gwamnoni 36 za su yi taro inda za su dauki matsaya game da cire tallafin fetur

- Za ayi wannan muhimmin zama ne ta kafafen yanar gizo a gobe Ranar Alhamis

- Kungiyar NGF ta bada wannan sanarwa ta bakin Abdulrazaque Bello-Barkindo

Gwamnonin jihohi 36 a Najeriya a karkashin kungiyarsu ta NGF za su yi wani zama na musamman a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa manyan makasudan zaman da za ayi su ne batun tallafin man fetur da rigakafin annobar cutar Coronavirus.

Gwamnonin sun bayyana wannan ne a wani jawabi da su ka fitar ta bakin shugaban yada labarai na kungiyar NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo.

Mista Abdulrazaque Bello-Barkindo ya ce za ayi wannan taro ne a ranar Alhamis ta kafofin yanar gizo

KU KARANTA: Farashin litar man fetur zai iya kai N185-N200 a Najeriya

Bello-Barkindo ya ce gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin tallafin fetur zai yi wa abokan aikinsa jawabi a taron.

Malam El Rufai zai tattauna game da sha’anin jigilar fetur kafin gwamnonin su dauki wata matsaya.

Shi kuma gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da annobar COVID-19 na NGF zai yi bayani game da rigakafin cutar.

Sanata Ifeanyi Okowa zai yi wa takwarorinsa bayanin inda aka kwana wajen raba maganin cutar.

KU KARANTA: Yakin Boko Haram ya na daf da zuwa karshe – COAS, Attahiru

Gwamnonin Jihohi 36 za su yi zama na musamman game da sha’anin farashin fetur
Kungiyar NGF a wajen taro
Asali: UGC

Shugaban kungiyar NGF, gwamna , Kayode Fayemi na jihar Ekiti, zai gabatar da rahoton zamansu da shugabannin da ke kula da jami’o’in jihohi na kasa.

A cewar Bello-Barkindo, gwamnoni za su ji aikin da kungiyar matan gwamnonin kasar su ka yi, sannan NDLEA da DFID za su gabatar da rahotanni a taron.

A makon jiya ne hukumar mai kula da farashin mai watau PPPRA ta bada sanarwar cewa an samu sauyi a kan kudin fetur, ta ce farashin lita ya kai N212.

Daga baya Timipre Sylva ya ce farashin man fetur ba zai canza ba har sai zuwa lokacin da gwamnati ta kammala tattauna wa da kungiyoyin kwadago.

Ministan harkokin mai, Timipre Sylva, ya ce babu wani kari da aka yi wa farashin litar man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng