Ba mu cikin kasar Biyafarar nan – Kungiyoyin Neja-Delta su na ta yi wa Dokubo Asari raddi

Ba mu cikin kasar Biyafarar nan – Kungiyoyin Neja-Delta su na ta yi wa Dokubo Asari raddi

- Kungiyoyi a Jihohin Ribas da Akwa Ibom sun nesanta kansu daga Dokubo Asari

- A makon nan ne ake jin cewa Dokubo Asari ya kafa sabuwar tafiyar ‘Yan Biyafara

- Ikwerre Peoples Congress, Southsouth Elders’ Forum, da PANDEF sun ce ban da su

Manyan jihar Ribas da wasu matasan yankin Neja-Delta sun ce babu ruwansu da ikirarin da tsohon tsagera, Alhaji Mujaheed Asari Dokubo, ya ke yi.

Ikwerre Peoples Congress ta ce surutan da Asari Dokubo yake yi ya ci karo da hakkin Bil Adama domin an cusa su cikin tafiyar Biyafara da karfi da yaji.

The Nation ta rahoto kungiyar IPC tana cewa Ikwere da yankunan Neja-Delta ba su cikin Biyafara.

Shugaban kungiyar IPC, Livingstone Wechie, ya ce: “Domin a sani, Ikwerre kasa mai zaman kanta a Najeriya wanda ta ratsa Duniya, kuma ba ta yi wa wata gundumar kabilanci mubaya’a ko da wani irin suna."

KU KARANTA: Kiristocin Arewa za su samu mafaka a Biyafara - Nnamdi Kanu

Babu tabas, kasar Ikwerre ta na cikin mafi girman kabilu a Najeriya inji Livingstone Wechie.

“Saboda haka, kungiyar IPC a matsayinta da sauran kungiyoyi na kasar Ikwerre, su kadai ne su ke da hurumin ta-cewa a game da matsayar mutanenta.”

“A wannan gaba, mu na jaddada cewa ko da kakannin Asari (Dokubu) sun fito ne daga kasar Ikwerre, yayin da shi kuma Asari mutumin Neja-Delta ne, bai da damar da zai yi magana a madadin Ikwerre ko kasar Neja-Delta da kansa ko a karkashin wasu ‘yan kanzagi.”

Kungiyar ta ce ta na fafutukar kare hakki da dukiyoyin kasarsu, amma ba ta tare da Asari Dokubo a nan.

KU KARANTA: Ibo ba su bukatar mulkin Najeriya - Shugaban IPOB

Ba mu cikin kasar Biyafarar nan – Kungiyoyin Neja-Delta su na ta yi wa Dokubo Asari raddi
Mujaheed Dokubo Asari Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Kasar Ikwerre ta fi karfin wani ya fito ya na magana a madadinta. Asari Dokubo ko wani bai isa ya kakaba manufar kansa a kan mutanenmu ba inji Wechie.

Wannan shi ne ra’ayin Southsouth Elders’ Forum (SEF) kamar yadda Sarah Igbe ta bayyana, ta ce har kungiyar PANDEF ba ta goyon bayan ikirarin na Asari.

Ita ma kungiyar matasan Ibibio Youth Council (IYC), ta Akwa Ibom ta ce ba ta tare da tsageran.

A farkon makon nan ku ka ji cewa tsohon tsageran Neja-Delta, Asari Dokubo ya farka, ya na neman ya dawo da ta’adin fafatukar Biyafara a Najeriya.

Asari Dokubo ya ce kungiyar Biafra Customary Government da ya ke jagoranta za ta kafa Gwamnoni da za su karbe Jihohin da ke yankin Kudu.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng