Labari mai Daɗi: Ɗalibai mata biyu da aka sace a Jami'ar OOU sun kuɓuta
- Wasu ɗalibai mata guda biyu da masu garkuwa suka sace a Jami'ar Olabisi Onabanjo sun kuɓuta.
- A ranar Lahadin data gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka sace ɗaliban a gaban gidan kwanan su dake Ayetoro, jihar Ogun
- Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Ogun, DSP, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sakin 'yan matan biyu
Ɗalibai mata guda biyu dake karatu a jami'ar Olabisi Onabanjo (OOU) waɗanda aka sace ranar Lahadi da daddare sun samu kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.
KARANTA ANAN: NDDC ta fallasa Gwamnonin N/Delta 9, an ba kowace Jiha N100m a matsayin tallafin COVID-19
Ɗaliban Adeyemo Precious da kuma Oyefule Abiola na karatu a ɓangarori daban dana juna a jami'ar, kuma an sace su ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe tara na dare lokacin da maharan suka kai farmaki layin Igbole Aibo dake Ayetoro, karamar hukumar Yewa.
Gwamanan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da dawowar ɗaliban.
Sa'ilin da yake tabbatar da kuɓutar da ɗaliban, gwamnan yace:
"Muna farin cikin sanar da cewa mun kuɓutar da Precious Adeyemo da kuma Abiola Oyefule, Dukkan su ɗaliban OOU ne da aka sace kwanan nan a Ayetoro."
"Muna godiya da jinjina ga rundunar 'yan sandan jihar mu da kuma sauran jami'an tsaro da suka taimaka wajen ganin ɗaliban sun koma gida cikin ƙoshin lafiya," inji gwamnan.
Rundunar 'yan sanda ta bakin mai magana da yawun ta, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sakin ɗaliban.
KARANTA ANAN: Kudiri zai ba Majalisa karfin sauke Shugaban kasa idan ya yi taurin-kan amsa gayyatarsu
Sai dai, babu wani cikakken bayani kan ko an biya kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban ko ba'a biya ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A ranar Talata da safe, gwamna Abiodun ya bawa jami'an tsaron jihar umarnin kuɓutar da ɗaliban biyu daga hannun maharan kuma su tabbata dai waɗanda aka sace din ba'a cutar dasu ba.
A wani labarin kuma Hukumar JAMB Ta Tuhumi Ma'aikatanta biyu Kan Badaƙalar Gurbin Shiga Jami'a.
Waɗanda ake tuhuma ɗin sun amsa laifin su na amsar cin hanci a hannun wasu iyayen yara 4
Shugaban JAMB yace basani ba sabo akan duk wanda aka kama da cin hanci a hukumar ko waye shi.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.
Asali: Legit.ng