Buhari ya sallami darakta janar na hukumar NiMet, yayi muhimman nade-nade 3

Buhari ya sallami darakta janar na hukumar NiMet, yayi muhimman nade-nade 3

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki shugaban hukumar binciken yanayi (NiMet), Farfesa Sani Mashi

- Ya maye gurbinsa da Bako Mansur Matazu, wanda kafin nan shine shugaban cibiyar binciken yanayi

- Duk da sallamar Mashi da shugaban kasan yayi, ya kamata wa'adin mulkinsa ya kare ne a Janairun 2022

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami darakta janar na hukumar binciken yanayi (NiMet), Farfesa Sani Mashi.

Wa'adin Mashi zai cika ne a watan Janairun 2022 amma shugaban kasa ya maye gurbinsa da Bako Mansur Matazu.

Matazu yana da digirin digirgir a fannin Geography kuma mamba ne a kungiyoyi kamar haka: Nigerian Environmental Society, African Forestry Forum, Nigerian Meteorological Society, the Climate Change Network, Nigeria and the renewable Energy and Energy Efficiency, Nigeria (REEN).

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kafin yi mishi nadin shugabancin NiMet, shine darakta janar na cibiyar bincike ta ilimin yanayi.

KU KARANTA: Ka daina jan kunnen 'yan bindiga da Turanci, kayi da yarensu, Shehu Sani ga Buhari

Buhari ya sallami darakta janar na hukumar NiMet, yayi muhimman nade-nade 3
Buhari ya sallami darakta janar na hukumar NiMet, yayi muhimman nade-nade 3. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kyaftin Modibbo Alkali Mahmud a matsayin sabon shugaban kwalejin koyon tukin jirgin sama, NCAT, Zaria.

Hakazalika, shugaban kasar ya nada Injiniya Akin Olateru a matsayin kwamishina kuma shugaban hukumar AIB

KU KARANTA: NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya

A wani labari na daban, Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar nan da wa'adin da yake basu tare da jan kunne.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam'iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

A ranar Juma'a ne jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kutsa kwalejin harkar noma da gandun dabbobi dake Kaduna suka kwashe dalibai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel