Tsohon gwamnan Imo Rochas Okrocha ya gana da Obasanjo a Abeokuta

Tsohon gwamnan Imo Rochas Okrocha ya gana da Obasanjo a Abeokuta

- Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai ci a yanzu, Rochas Okorocha ya gana da tsohon shugaban kasa OLusegun Obasanjo

- Sanatan da ke wakiltar Imo ta yamma ya gana da Obasanjo ne a dakin karatun OOPL dake Abeokuta

- Ya bayyana cewa dole ne su rinka kaima dattawan kasa ziyara daga lokaci zuwa lokaci.

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta jihar Ogun ranar Litinin da yamma.

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023: Wani ɗan majalisa ya roƙi gwamnan Rivers Wike ya fito takarar shugaban ƙasa

Okorocha mai wakiltar Imo ta yamma a majalisar dattawan Najeriya ya gana ne da Obasanjo a gidansa dake cikin harabar dakin karatu na 'Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL)' a Abeokuta.

Tsohon gwamnan wanda yake harin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 ya bayyana hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta na twita.

Ya nuna muhimmancin tattaunawa da dattijan kasa daga lokaci zuwa lokaci domin cigaban kasa.

Tsohon gwamnan Imo Rochas Okrocha ya gana da Obasanjo a Abekuta
Tsohon gwamnan Imo Rochas Okrocha ya gana da Obasanjo a Abekuta Hoto: @RealRochas
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta

Rochas ya rubuta a shafinsa:

"Yau na kai ziyarar girmamawa ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a dakin karatu na Obasanjo dake Abeokuta, jihar Ogun... Dole ne mu dinga tuntubar dattijan kasa daga lokaci zuwa lokaci domin ciyar da kasar nan gaba"

Daily Trust ta ruwaito cewa satin da ya wuce Okorocha ya bayyana kwarin guiwar sa na tsayawa takara da lashe takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

Okorocha wanda yayi magana a Abuja sanda wasu matasa suka kai masa ziyara.

Tsohon gwamnan yana daga cikin wadanda suka kafa jamiyya mai mulki ta APC, ya bayyana cewa Najeriya na cikin wani hali na matsi saboda tabarbarewar rashin tsaro.

A wani labarin kuma Manyan motocin alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa sun janyo cece-kuce.

Hotunan tawagar motocin da shugaban kungiyar Miyettei Allah ke yawo dasu sun janyo cece-kuce.

Kamar yadda aka gani, shugaban kungiyar na yawo da motocin alfarma tare da 'yan sanda dake tsaron lafiyarsa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Source: Legit

Online view pixel