Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Najeriya

Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Najeriya

- Kungiyar darikar Tijjaniya ta musanta nadin da ake yadawa tayi wa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi

- Kamar yadda Sheikh Mahi Nyass ya sanar, ana nadi ne bayan malamai sun tantance mutum kuma Khalifatul Arrm ya bashi takardar shaida

- A cewar Sheikh Mahi, Tsohon sarkin Kano bai nuna bukatar kujerar ba balle a kai ga tantancesa har ayi masa nadin

Dariqar Tijjaniya ta musanta baiwa tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II shugabancinta na Najeriya.

Sheikh Mahi Nyass, shugaban darikar Tijjaniya na duniya wanda ake kira da Khalifatum Arrm, ya bayyana hakan yayin da yayi jawabi ga manema labarai a Sokoto.

Jaridar The Punch ta wallafa cewa, Nyass, wanda shine da kuma magajin Shehu Ibrahim Nyass, yace in har za a yi nadi ana tantancewa sannan a zaba daga cikin mabiyanta na Najeriya da Senegal.

KU KARANTA: NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya

Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Afrika
Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Afrika. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

"Irin wadannan hukunci ana tattaunawa ne sannan a amince kafin a sanar. Bayan an zaba mutum, akwai wasikar amincewa daga malamai wacce Khalifatul Arrm zai saka hannu kuma ya mika ga wanda aka nada," Nyass yace.

Ya ce Sanusi bai nuna bukatar kujerar ba kuma shugabannin basu riga sun fitar da tsarin da za a bi ba wurin wannan nadin.

"Hadin kan 'yan kungiya yana da amfani kuma ina kira ga kungiyar da ta mayar da hankali wurin bauta, kara dankon zumunci da kaunar juna," yace.

Sheikh Ibrahim Dahiru-Bauchi, ya kwatanta labarin nadin Sanusi da labarin bogi.

KU KARANTA: Kano: Allah ya yi wa gogaggen dan siyasa kuma fitaccen dattijo, Dangalan, rasuwa

A wani labari na daban, fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Maulidin kasa dake jihar Sokoto sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kankara zuwa Sheme dake jihar Katsina.

Majiyoyi da dama a yankin sun sanar da cewa basu san yawan wadanda aka sace ba yayin da jami'an 'yan sanda suka ce babu wanda aka sace.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wasu majiyoyin sun ce an sace mutum 70 inda wasu suka ce fasinjoji 50 ne aka yi awon gaba dasu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel