Covid-19: NAFDAC tayi kakkausan gargaɗi a kan allurar rigakafin bogi

Covid-19: NAFDAC tayi kakkausan gargaɗi a kan allurar rigakafin bogi

- Hukumar kula da ingancin abinci da kuma kwayoyi ta ƙasa (NAFDAC) ta gargaɗi 'yan Najeriya kan allurar rigakfin Korona ta bogi

- Hukumar ta kuma gargaɗi 'yan Najeria ta su guji faɗawa hannun mugayen mutane musamman ta yanar gizo wato (Online)

- Ana sa ran za'ayi wa jami'an lafiya allurar rigakafin cutar korona su 5,000 Yau a Babban Birnin tarayya, Abuja

Hukumar kula da ingancin abinci da kwayayo ta kasa (NAFDAC) ta gargaɗi yan Nijeriya da kakkausan murya kan rigakafin cutar korona ta bogi.

NAFDAC ta ƙara gargadin 'yan ƙasa da su guji siyan rigakafin musamman ta yanar gizo wato (online) don gudun faɗawa hannun munanen banza, Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun

Hukumar ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su bayyana duk wani wanda yayi kokarin karkatar da allurar rigakafin da aka kawo Najeriya domin yan ƙasa.

Shugaban hukumar, Prof Mojisola Adeyeye, tayi wannan gargaɗin a wani saƙo da mai kula da al'amuran labarai na hukumar, Sayo Akintola, ta fitar.

A Cewarta: "Yakamata mutane su kula da masu ɗauke da rigakafin bogi da kuma masu yaudarar mutane da rigakafin dama sauran abubuwa."

Ana sa ran za'a yiwa jami'an lafiya kimanin su 5,000 allurar rugakafin korona a babban birnin tarayya Abuja, yau Litinin da kuma Talata.

Covid-19: NAFDAC tayi kakkausan gargaɗi a kan allurar rigakafin bogi
Covid-19: NAFDAC tayi kakkausan gargaɗi a kan allurar rigakafin bogi Hoto:.@NafdacAgency
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Sabon shugaban hafsun Sojojin Najeriya ya ce an kusa gama yakin Boko Haram

Za'a yima jami'an lafiya na sahun farko allurar ne a Asibitin Asokoro, dake Abuja, inda ministan Abuja zai ƙaddamar da fara rigakafin.

A lokacin da yake magana da manema labarai, sakataren riƙo na hukumar lafiya na sakateriyar Abuja, Dr Mohammed Kawu, ya bayyana cewa:

"A ranar Litinin zamu fara yiwa jami'an lafiya ne kaɗai, Muna fatan muyi musu duka a wannan rana ko kuma mu haɗa da ranar talata. Bayan wannan zamu sanar da waɗanda zamu yima na gaba."

"A asibitocin da muke dasu a Abuja, muna da ma'aikata 5,000, amma bamu haɗa da adadin ma'aikatan asibitoci masu zaman kansu ba," a cewarsa.

A wani labarin kuma Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta

A wani yanki, mazauna da masugadin makabarta sun koka kan yadda ake sace allunan alama.

Sun bayyana zarginsu ga 'yan gwan-gwan dake tsince-tsincen karafa, su kuwa sun musa hakan.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel