'Yan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami'a biyu, sun nemi a basu 50 miliyan
- Wasu 'yan bindiga sun sace ɗalibai mata guda biyu a jami'ar Olabisi Onabanjo dake jihar Ogun
- An bayyana cewa an sace ɗaliban ne a gaban gidan kwanan su dake ƙaramar hukumar Yewa ta Arewa, Jihar Ogun
- 'Yan bindigan sun tuntuɓi iyalan waɗan da suka kama, kuma sun ce sai an basu 50 miliyan sannan zasu saki ɗaliban
Wasu 'yan bindiga sun sace ɗalibai mata guda biyu dake karatu a jami'ar Olabisi Onabanjo University (OOU) dake karamar hukumar Yewa ta Arewa, jihar Ogun.
Waɗan da aka sace ɗin sune; Adeyemo Precious da kuma Oyefule Abiola dukkan su ɗaliban OOU ne dake karatu a fanni daban-daban.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an sace ɗaliban ne a gaban gidan kwanan su dake unguwar Ayetoro ranar Lahadi da daddare.
KARANTA ANAN: A karon farko, Fani-Kayode ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a Osun
Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunan ta, ta bayyana cewa 'yan bindigan sun nemi iyalan ɗaliban su biya kuɗin fansa 50 miliyan sannan su sake su.
Majiyar ta ƙara da cewa 'yan bindigar sun nemi iyalan ɗaliban ne ta hanyar amfani da wayoyinsu.
Da aka tambayi majiyar ko mutanen fulani makiyaya ne, sai suka ce ɗaliban ne suka yi magana da 'yan uwan nasu ba 'yan bindigan ba.
"Masu garkuwa da mutanen basu yarda sunyi magana da kowa ba, ɗaliban ne suka kira suka faɗi buƙatun. Bamu sani ba ko Yarbawa ne ko Fulani saboda iyalan waɗan da abun ya shafa basu yi magana da masu garkuwan ba," a cewar majiyar.
KARANTA ANAN: Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3
Lokacin da aka nemi me magana da yawun 'yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, yace yana taro ne, amma zayyi magana bayan ya fito daga taron.
Sai dai wata ƙungiya a ƙaramar hukumar Yewa ta yi kira ga gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, da ya umarci kwamishinan 'yan sanda ya dawo yankin Yewa ta Arewa don shawo kan lamarin.
Ƙungiyar tace ƙaramar hukumar ta Yewa na fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa:
"Bamu samun kulawar 'yan sanda tunda DPO ya mutu, kuma har yanzun ba'a turo sabon DPO ba a yankin. DCO dake riƙe da muƙamin baya bawa mutanen mu haɗin kai yadda ya kamata. Muna roƙon hukumomi su canza mana wannan DCO."
Anashi ɓangaren, shugaban ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa reshen jihar, Mr. Adeyemi Samson, ya roƙi gwamnan jihar da ya tabbatar da tsaron lafiyar ɗaliban jihar ta Ogun.
A wani labarin kuma NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya.
Kamar yadda hukumar ta sanar a wata takarda da ta fitar, jami'o'in na bada shaidar digiri ne cikin watanni kalilan da fara karatu.
Hukumar ta shaidawa shugabannin dukkan sansanonin NYSC na kasar nan da kada su yi wa daliban rijista.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng