NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya

NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya

- Hukumar NYSC ta haramtawa daliban da suka kammala daga jami'o'i 8 na kasashen Kamaru, Nijar da Benin bautar kasa

- Kamar yadda hukumar ta sanar a wata takarda da ta fitar, jami'o'in na bada shaidar digiri ne cikin watanni kalilan da fara karatu

- Hukumar ta shaidawa shugabannin dukkan sansanonin NYSC na kasar nan da kada su yi wa daliban rijista

A kalla jami'o'i takwas ne dake jamhuriyar Benin, Nijar da Kamaru hukumar NYSC ta hana daliban Najeriya da suka yi digiri yin hidimar kasa a Najeriya.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, da yawa daga cikin jami'io'in wadanda ake kira da jami'o'in Kwatano, suna bada shaidar digirinsu ne bayan watanni kadan da fara karatu.

Duk da shugabannin hukumar basu bada dalililinsu na daukan wannan matakin ba a wata takarda da ta fitar a ranar 5 ga watan Maris ga shugabannin sansanonin bautar kasar dake fadin kasar nan, ta sanar da cewa kada su karba daliban da suka dawo daga wadannan jami'o'in.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta wanke matar da ake zargi da sheke mijinta ta hanyar yi wa mijinta allurar guba

NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya
NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya. Hoto daga @officialnyscng
Asali: Twitter

Ga jerin sunayen jami'o'in da kasar da suke:

1. Al-Nahda International University (Jamhuriyar Nijar)

2. Ecole Superieur Sainte Felicite ( Jamhuriyar Benin)

3. Ecole Superieur D Administration et DEconomics (Jamhuriyar Benin)

4. Ecole Superieur DEnseignement Professionelle Le Berger – ESEP Le Berger (Jamhuriyar Benin)

5. Ecole Superieur St. Louis DAfrique (Jamhuriyar Benin)

6. Institute Superieur de Comm.

7. Dord Et De Management – ISFOP (Jamhuriyar Benin)

8. International University, Bamenda (Cameroon)

A wani labari na daban, Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tara taron masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.

A makonni kadan da suka gabata ne aka dinga rikici a kan zargin da ake wa makiyaya da kashe-kashe tare da garkuwa da mutane a kudu maso yammacin kasar nan.

A watan Janairun da ta gabata ne Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bukaci makiyaya da su bar dukkan dajikan jiharsa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel