A karon farko, Fani-Kayode ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a Osun

A karon farko, Fani-Kayode ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a Osun

- Femi Fani-Kayode ya yi martani a kan kisan gillar da aka yi wa wasu 'yan gida daya har mutum 6

- Tsohon ministan sufurin jiragen saman yace babu dalilin da zai sa ba za a kushe wannan harin ba

- Fani-Kayode ya jaddada cewa ba zai taba bada hakuri ba saboda ya kushe wannan kisan da aka yi wa iyalan

Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode a ranar Litinin, 15 ga watan Maris ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a jihar Osun.

Fani Kayode wanda ya nuna damuwarsa a kan aukuwar mummunan lamarin, ya ce an haresu ne ganin basu da yadda zasu kare kansu.

Ya sanar da hakan ne a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter inda yace kisan gillar bai dace ba kuma babu jarumta a ciki.

KU KARANTA: Kano: Allah ya yi wa gogaggen dan siyasa kuma fitaccen dattijo, Dangalan, rasuwa

A karon farko, Fani-Kayode ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a Osun
A karon farko, Fani-Kayode ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a Osun. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

KU KARANTA: Rikicin manoma da makiyaya: Ka gaggauta yin taron tsaron kasa, Tinubu ga Buhari

Jigon jam'iyyar PDP din yace zaman dan Adam Bafulatani bai dace a ce za a dinga kashe shi ba.

A yayin caccakar wadanda suka kushe takardar da ya fitar, Fani-Kayode yace ba zai taba goyon bayan kisan jama'a ba, ba tare da laifin zaune ba balle tsaye. Yace banbancin addini ko kabila ba zai sa ya goyi bayan hakan ba.

A wani labari na daban, fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Maulidin kasa dake jihar Sokoto sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kankara zuwa Sheme dake jihar Katsina.

Majiyoyi da dama a yankin sun sanar da cewa basu san yawan wadanda aka sace ba yayin da jami'an 'yan sanda suka ce babu wanda aka sace.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wasu majiyoyin sun ce an sace mutum 70 inda wasu suka ce fasinjoji 50 ne aka yi awon gaba dasu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Online view pixel