'Kaicon ka': Shekau ya caccaki Sheikh Gumi saboda tattaunawa da 'yan bindiga

'Kaicon ka': Shekau ya caccaki Sheikh Gumi saboda tattaunawa da 'yan bindiga

- Shugaban 'yan ta'addan Boko Haram ya tura sako ga Sheikh Gumi da minista Dr Isa Ali Pantami

- Ya caccaki Sheikh Gumi saboda zaman tattauna da yake da 'yan bindiga a wasu sassan kasar

- Ya gargade su tare da kiransu da cewa, su koma ga Allah su bar Demokradiyya kasacewarta kafirci in ji shi

Shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya caccaki malamin addinin Islama da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, saboda tattaunawa da 'yan bindiga.

Kwanan nan Gumi ya shiga rangadi zuwa maboyar ‘yan bindigan dake dauke da muggan makamai a dazuka domin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da masu tada kayar bayan.

Zagayen malamin ya jawo maganganu daban-daban a tsakanin ‘yan Nijeriya, inda mutane da yawa, ciki har da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, suka yi Allah wadai da matakin.

Amma a cikin wani faifan murya da ya kai tsawon awa 1 da mintuna 55, wanda aka samo daga jaridar Daily Nigerian, Shekau ya ce Gumi na daga cikin wadanda suke yin barna da ganganci.

KU KARANTA: Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje

'Kaicon ka': Shekau ya caccaki Sheikh Gumi saboda tattaunawa da 'yan bindiga
'Kaicon ka': Shekau ya caccaki Sheikh Gumi saboda tattaunawa da 'yan bindiga Hoto: Observers Times
Asali: UGC

“Haba Ahmad Gumi! Haba Ahmad Gumi, yanzu kana yawo, kana tattaunawa da Fulani, kuma kana tunanin kana bautawa Allah.

“Saboda kawai ana ce maka Dokta ko Sheikh? Kaiconka Ahmad Gumi,” inji shi.

Ya kawo maganar sura ta 7 aya ta 175 na Alkur'ani, shugaban 'yan ta'addar ya ce game da Gumi: "Kuma ka ba su labarin (ya Annabi) wanda muke bai wa ayoyin Mu, sai ya yi watsi da su, sai Shaidan ya kama shi, kuma ya zama karkatacce.”

Shekau ya kuma zargi Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya, wanda malamin addinin Musulunci ne, saboda ya shiga gwamnati a karkashin tsarin dimokiradiyya.

“A gare ku (Gumi) da wasu irin su Pantami, menene ma minista, huh? Kuma har yanzu malami ne? Ku tambayi kanku! Ya ku malamai masu dandana dandanon mulki da iko, ku tambayi kanku,” in ji shi.

“Dukkanku kun san dimokiradiyya akidar yahudawa da kiristoci ne, me yasa ba ku bar gwamnati ba?

“Duk da sanin gaskiya, kuna amfani da Alkur’ani wajen wa’azin dimokiradiyya. Me ya sa haka?”

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace wata yarinya 'yar shekara 18 a cikin gidan mahaifinta a jihar Kebbi

A wani labarin, Yayin da sojoji ke tsananta yaki da masu tayar da kayar baya a Borno, babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, da shugabannin hafsoshi, sun isa Maiduguri, a karo na biyu a cikin wata daya don tantance halin da ake ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yiwa sojojin jawabi, a ranar Asabar, a hedkwatar "Operation Lafiya Dole" a Maiduguri, Irabor ya yaba musu saboda nasarorin da aka samu.

Ya kuma yaba musu kan jajircewa da juriya, ya kara da cewa akwai wani umarni da Shugaban kasa da Babban Kwamanda ya bayar wanda dole ne a cika su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.