Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun harbe wasu masu garkuwa da mutane a Abuja

Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun harbe wasu masu garkuwa da mutane a Abuja

- Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar bindige wasu masu garkuwa da mutane biyu har lahira a Unguwar Hausawa dake Abuja

- Wani shaida ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun farma wasu gidaje a Unguwar har sukayi awon gaba da mutum huɗu

- Shugaban ƙaramar hukumar da lamarin ya faru ya tabbatar da kisan da akayi ma masu garkuwan biyu

Yan Sanda sun bindige masu garkuwa da mutane mutum biyu a Anguwar Hausawa, a yankin Naharati a karamar hukumar Abaji, dake Abuja.

Daily trust ta ruwaito cewa an kashe  masu garkuwa da mutanen ne yayin wata musayar wuta da yan sandan sukayi da maharan tare da gudummuwar jami'an sa kai na unguwar.

Wani mazaunin unguwar mai suna Suleiman yace misalin karfe daya na daren Lahadi, yan bindigan suka shiga wasu gidaje a Anguwar Hausawa.

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC tayi wani babban Kamu a jihar Ogun

Yace kafin zuwan jami'an tsaro, yan bindigan sun kutsa cikin wasu gidaje inda suka tafi da mutane hudu.

Mutane hudun da aka sace sune Abdullahi Umar, Abdulkarim Yusuf, Abubakar Umar da wani yaro dan shekara 13 Abdulrahman Isah.

"Sun fara harbe-harbe a cikin iska domin firgita mazauna unguwar bayan sun dauke mutane hudun" mutumin yaa bayyana

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya ya tabbatar da satar mutanen da kuma kisan yan garkuwar mutum biyu.

KARANTA ANAN: Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna

Wakilin Daily trust da ya ziyarci ofishin yan sandan ya ganewa idonsa gawarwakin masu garkuwa da mutanen a shimfide a kasa.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun garzaya domin daukar hotuna da bidiyon gawarwakin.

Daga cikin abubuwan da aka samu a wajen su sun hada da layukan waya, layoyi da kuma wayoyi.

Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar yan sandan birnin tarayya, ASP Maryam Yusuf ta tabbatar da satar da kuma kisan mutanen guda biyu.

Tace yan sanda sun dakile harin, inda ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen da suka samu raunika sun rasu yayin da aka kaisu asibiti.

A wani labarin kuma Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

Kansilan ya dauki hadimai sama da mutum 10 domin taimaka masa a gudanar da aikinsa

Kansilan ya bayyana hakan da yunkurin samar da ji da gani daga wajen talakawa da halin da suke ciki.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwanan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano. Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel