An kama gurbatattun kwayoyin magani na biliyan 6 a Jihar Kano

An kama gurbatattun kwayoyin magani na biliyan 6 a Jihar Kano

- A jihar Kano, an kame gurbatattun kwayoyin magunguna na sama da biliyan 6 a cikin shekaru kadan

- Hukumar da ke da hakkin kamen tace jihar Kano ta sauka daga matsayin ta farko a tu'ammuli da kwayoyi

- Hakazalika, hukumar tace tsarkake Kano daga kwayoyin daidai yake da tsarkake wasu kasashen Afrika

Kwamitin da ke yaki da gurbatattun kwayoyi da abinci a Jihar Kano ya ce ya kwace tare da lalata kwayoyin magani na bogi da suka kai darajar naira biliyan shida a cikin shekara tara da suka gabata.

Shugaban kwamitin Gali Sule ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar kungiyar 'yan jarida ta Kano ranar Asabar, kamar yadda NAN ya ruwaito.

KU KARANTA: Yanzun nan: An yi bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga a filin jirgin sama na jihar Kaduna

An kama gurbatattun kwayoyin magani na biliyan 6 a Jihar Kano
An kama gurbatattun kwayoyin magani na biliyan 6 a Jihar Kano Hoto: Mankind Pharma
Asali: UGC

A cewarsa, tun bayan kafa kwamitin a 2012 sun kama da kuma lalata kwayoyi na bogi a wurare daban-daban kusan 20 na jihar.

Shugaban ya ce yanzu haka Kano ta sauko daga matsayi na 1 a jerin jihohin da suka fi ta'ammali da kwayoyin bogi zuwa mataki na 6.

"Idan aka kubutar da Kano daga ta'ammali da miyagun kwayoyi an kubutar da kasashe da yawa a Afirka saboda kasashe kamar Nijar da Chad da Sudan suna sayen kwayoyi ne daga Kano." in ji shi.

KU KARANTA: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

A wani labarin daban, Hukumar NAFDAC mai sa ido kan ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta ce ana nan ana ta gwajin magungunan gargajiya 14 a kasar don samar magani kan kwayar cutar Korona, BBC Hausa ta ruwaito.

Shugabar hukumar Farfesa Adeyeye ta ce magungunan tuni sun wuce matakin farko na gwaji, kawo yanzu kuma ana duba yiwuwar amfani da su kan magance kwayar cutar ta Korona.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel