An garƙame makarantar da aka sace ɗalibai a Kaduna har sai baba ta gani
- An kulle makarantar FCFM dake afaka, Jihar kaduna har sai baba-ta-gani bayan sace ɗaliban makarantar 39 a daren Alhamis ɗin data gabata
- A baya bayan nan ne dai, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yasha alwashin kawo ƙarshen satar mutane a ƙasar
- 'Yan bindigar sun saki bidiyon dake nuna halin da ɗaliban ke ciki jiya
An sanar da kulle makarantar FCFM dake Afaka a jihar Kaduna, har sai baba-ta-gani, hakan ya biyo bayan sace ɗaliban makarantar da wasu 'yan bindiga sukayi.
An kulle makarantar ne bayan farmakin da wasu 'yan bindiga daɗi suka kai makarantar har sukayi awon gaba da ɗalibai 39. Channels TV ta ruwaito
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kuɓutar da ɗalibai 180 kuma sun koma makarantar tasu har sun haɗu da iyalansu.
KARANTA ANAN: Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno
A halin yanzu, ɗaliban dake hannun 'yan bindigar sunyi kira da akawo musu ɗauki a wani faifan bidiyo da aka saki jiya.
A hangi ɗaliban da aka sace na shan duka daga hannun masu garkuwa dasu, a lokacin da suke roƙon gwamnati da ta kuɓutar dasu a bidiyon.
An ga ɗaliban a cure wuri ɗaya kuma a zaune karƙashin bishiyoyi, ga kuma wasu mutane ɗauke da bindigu a tare dasu, wasu daga cikin su na sanye da kayan sojoji.
KARANTA ANAN: An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue
Gwmnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin ɗaliban da aka sace sunkai 39.
Bayan wannan mummunan farmakin, jami'an tsaro sunce suna iya bakin ƙoƙarinsu dan ganin sun kuɓutar da ɗaliban.
Kwanan nan, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yasha alwashin kawo ƙarshen garkuwa da mutane da akeyi a faɗin ƙasar.
Saidai, 'yan bindiga sunyi awon gaba da ɗalibai guda 39 a Arewa maso yammacin kasarnan, jihar Kaduna ranar alhamis da daddare.
Jami'an soji sunyi ƙoƙarin ceto mutum 180 bayan musayar wuta a makarantar ta gandun daji dake Mando, Babban birnin jihar Kaduna.
A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun kwashe 'yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto
Miyagun 'yan bindiga sun kaiwa fasinjojin dake kan hanyar zuwa Maulidin kasa a Sokoto hari
An gano cewa 'yan bindigan sun kwashe fasinjoji masu yawa a hanyar Kankara zuwa Sheme
Asali: Legit.ng