Kasaitattun fadar sarakuna 6 a Najeriya da kyawawan hotunansu
Sanannen abu ne idan aka ce fada ce wurin zaman sarakuna, wuri ne kuma na samun ilimin al'adun jama'a.
Najeriya tana kunshe da fadar sarakuna masu tarin yawa, amma Legit.ng ta kawo muku bayani da hotunan kasaitattun fadar sarakuna shida da suka fi kyau a kasar nan.
1. Fadar Ooni na Ife
Fadar Ooni na Ife na bayyana hazaka wurin yadda aka tsara ginin kuma duk wanda ya ziyarci fadar zai diba daga kogin ilimi da ke dankare a fadar.
2. Gidan Rumfa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ce fadar sarkin Kano. Ziyartar Gidan Rumfa tamkar zuwa ne ka duba tsarin gine-ginen mutanen baya.
An gina fadar a karshen karni na 15 cike da tarihin kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal
3. Fadar Oban Benin
Wannan ce fadar Oba na Benin kuma ta kasance wurin da ke jan hankalin masu ziyara. Jama'a idan suka kai ziyara suna ganin kotun Oba, saurauniyarsa Harem da gidan tarihin fadar wanda ke cike da kayan tarihi na masarautar Benin.
4. Fadar sarkin Zazzau
Fadar tana da kyakyawan ginin wanda aka yi wa adon sarauta. Wuri ne da masu sha'awar daukar hoto kan tsaya su kashe kala.
5. Fadar sarkin Musulmi
Duk wanda ya ziyarci fadar sarkin Musulmi zai gane tarihin masarautar Sokoto. Wuri ne da ke cike da tarihi mai kayatarwa.
KU KARANTA: 'Yan ta'adda sun shiga Maiduguri, zakakuran sojin Najeriya sun yi musu 'dakan gumba'
6. Fadar Obi na Onitsha
Wannan fadar na bayyana zamanin kafin zuwan Turawa kuma tana dauke ne da tarihi na bukukuwa daban-daban na kasar.
A fadar, za ka iya samun gumakan sarakunan da suka gabata masu bada sha'awa. Duk wanda yake neman tarihin Onitsha, za a iya samunsa a fadar.
A wani labari na daban, sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli da sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Maigwari II, sun ce mutanensu sun biya daruruwan miliyoyi a matsayin kudin fansa ga 'yan bindiga.
Sun sanar da hakan ne yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 ga Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, The Nation ta wallafa.
Maigwari ya ce: "Abun takaici ne da tashin hankali ka ga 'yan bindiga 200 zuwa 300 dauke da makamai sun zagaye kauye suna kashe jama'a tare da karbe kudadensu. Jama'armu sun biya daruruwan miliyoyin naira a matsayin kudin fansa."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng