'Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Kaduna, sun kone gidaje da dama

'Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Kaduna, sun kone gidaje da dama

- Yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka a kananan hukumomin jihar Kaduna, sun kashe mutane bakwai

- Kwamishinan tsaron cikin gidan na jihar Kaduna, Mr Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis

- Samuel Aruwan ya ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya yi bakin ciki game da hare-haren ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu

Yan bindiga sun kai hare-hare a kananan hukumomin Igabi, Giwa da Chikun na jihar Kaduna inda suka halaka mutane bakwai suka raunta wasu da dama.

Kwamishinan harkokin gida da tsaro na jihar, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da ya fitar.

'Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Kaduna, sun kone gidaje da dama
'Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Kaduna, sun kone gidaje da dama. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A cewarsa, yan bindigan sun afka kauyen Gambi a karamar hukumar Igabi suna harbe-harbe a wani abu da ya yi kama da satar shanu inda suka kashe mutane hudu.

Wadanda aka kashe sune; Amiru Saidu, Yusha’u Mohammadu da Osama Abdulwahab, a cewar Samuel Aruwan.

DUBA WANNAN: Bayan haihuwar yara 5, matar manomi ta sake haifar masa ƴan biyar

Ya kara da cewa yayin harin, yan bindigan sun kone gidaje uku mallakar Mohammad Jibril, Salisu Ya’u da Idris Muhammad.

Ya kuma ce sun kona wata babban mota mallakar wani Umaru Saleh.

"Gaba daya sun sace shanu 20 mallakar wasu mazauna kauyen. A wani harin daban, yan bindiga sun kai hari kauyen Marte a karamar hukumar Giwa sun kashe wani Rabiu Haruna," in ji shi.

A garin Kuriga a karamar hukumar Chikun, yan bindigan sun kashe mutane biyu a hanyar Buruku da ta hade da karamar hukumar Birnin Gwari.

KU KARANTA: Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin Ibadan

Wadanda aka kashe sune Ibrahim Yahu Birnin Gwari da Haruna Usman.

Ya kuma ce wani Mansur Dada ya samu rauni yana asibiti.

Mr Aruwan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi bakin ciki da faruwar hare-haren ya yi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya bawa wadanda suka ji rauni sauki.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel