Buhari Ya Ƙaddamar Da Sabon Ginin Hukumar Raya Yankin Niger-Delta
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon ginin hukumar raya Niger-Delta
- Buhari ya ƙaddamar da ginin ne daga fadar sa dake Abuja, ta hanyar amfani da fasahar zamani 'Virtually'
- Ministan harkokin Niger-Delta Godswill Akpabio ya bayyana kammala ginin da gwamnati tayi da babban cigaba
Shugaba Buhari ya Ƙaddamar da sabon gini na zamani ga hukumar kula da raya yankin Niger-Delta wato NDDC.
An dai ƙadɗamar da wannan ginin na babbar cibiyar hukumar ne yau alhamis a Fatakwal shekaru 25 bayan aza harsashin ginin. The Nation ta ruwaito
KARANTA ANAN: Masu kira ga gwamnati ta kama ni kidahumai ne, Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani
Buhari wanda ya halarci taron da hukumar ta gudanar ta kafar zamani daga Abuja, ya jinjina ma ministan harkokin Niger-Delta wato Sanata Godswill Akpabio.
Shugaban ya jinjina ma ministan bisa irin jajircewar da yayi wajen kawo ƙarshen zaman hukumar a mazauni na haya da kuma bannar kuɗaɗe da ake yi dangane da hakan.
Shugaban yace mazaunin NDDC na yanzu ya kasance mallakin hukumar yankunan dake samar da mai da albarkatun ƙasa ne wato OMPADEC wanda hukumar ta dena aiki dashi tun bayan wasu yan gyare-gyare.
KARANTA ANAN: Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki
"A shekarar 2015, daga cikin manyan ƙudurorin gwamnatin mu na yaƙar rashawa, akwai wasu muhimman gyare-gyare da muka ɗauko, daga cikinsu kuwa harda gyara kafatanin hukumar ta NDDC don amfanin al'ummar yankin na Niger-Delta." inji Buhari.
"Domin cimma wannan buri, na sake sanya minista Akpabio don kulawa da harkokin gudarwar yadda ya kamata.
Sannan na sanya masu binciken ƙwaƙwaf su duba abubuwan da aka gudanar tun daga kafa hukumar a shekarar 2019 zuwa yanzu don tabbatar da anyi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata." Inji Buhari.
Buhari ya jinjina ma Akpabio kan wannan ƙoƙari, sannan ya buƙaci da suyi amfani da ƙuɗaɗen da ake fiddawa don biyan haya zuwa wasu ɓangarorin na daban.
"A yau zamu miƙa ma mutanen Niger-Delta sabon ginin cibiyar hukumar su. Bugu da ƙari, kuɗaɗen da ake amfani da su wajen biyan haya a baya zasu kasance an mayar da akalarsu zuwa wasu ɓangarorin." Buhari ya bayyana.
Shugaba Buhari ya ƙara da cewa:
"Na jinjina ma hukumar tare da duka ma'aikatanta wajen bamu haɗin kai don cimma wannan nasara. Kuma nayi farin ciki matuƙa wajen ganin yadda aka samu fahimtar juna tsakanin NDDC da zauren majalisar tarayya, ina fatan hakan ya zama silar ƙarin samun cigaba ga mutanen wannan yankin."
Ana shi ɓangaren, gwamnan jihar Imo wato Hope Uzodinma ya godewa shugaba Buhari dangane da ƙoƙarin ƙarasa wannan aiki da akayi.
Sannan ya alƙawarta cewa duka gwamnonin yankin su tara zasu cigaba da marama ƙudurorin cigaba da shugaban kasar zaizo da su.
A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sheke dan sanda, sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Benue
bindigan sun hallaka wani dan sanda tare da bankawa ofishi da motar 'yan sanda wuta
Rundunar 'yan sanda a jihar ta Benue ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bata bada bayani ba
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77
Asali: Legit.ng