Mun biya daruruwan miliyoyi a matsayin kudin fansa ga 'yan bindiga, Sarakuna
- Alhaji Ahmed Bamalli da Alhaji Zubairu Maigwari sun nuna damuwarsu a kan yadda ake sace jama'arsu
- Sarakunan Zazzau da na Birnin-Gwari sun bayyana cewa jama'arsu sun biya daruruwan miliyoyi ga 'yan bindiga
- Sarkin Zangon-Kataf, ya koka da yadda suke kaiwa 'yan sanda masu laifi amma ba a san yadda ake karewa dasu ba
Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli da sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Maigwari II, sun ce mutanensu sun biya daruruwan miliyoyi a matsayin kudin fansa ga 'yan bindiga.
Sun sanar da hakan ne yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 ga Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, The Nation ta wallafa.
Maigwari ya ce: "Abun takaici ne da tashin hankali ka ga 'yan bindiga 200 zuwa 300 dauke da makamai sun zagaye kauye suna kashe jama'a tare da karbe kudadensu. Jama'armu sun biya daruruwan miliyoyin naira a matsayin kudin fansa."
KU KARANTA: 'Yan ta'adda sun shiga Maiduguri, zakakuran sojin Najeriya sun yi musu 'dakan gumba'
Bamalli ya jinjinawa jami'an tsaro inda yace: "Muna da kalubale har yanzu a Zaria da Giwa saboda idan karfe 6 na yamma tayi ba a iya zuwa wasu yankuna. Wadannan wuraren suna da tsananin hatsari."
Sarkin Zangon-Kataf, Agwatyap, Dominic Yahaya, yace duk da yadda ake sace jama'a lokaci zuwa lokaci a yankinsa, kwamitin da ya kafa na neman zaman lafiya bai gaza ba.
Agwatyap, Dominic Yahaya yace: "Amma kuma idan muka kama masu garuwa da mutane muka kaiwa 'yan sanda, bamu san me suke musu ba. Za mu cigaba da neman zaman lafiya."
KU KARANTA: Bidiyon sankama daloli: Ganduje ya bukaci sauya rantsuwa da shaidu a gaban kotu
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa 'yan bindigan Zamfara watanni biyu to mika makamai, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da yammacin Talata.
Matawalle yace shugaban kasan ya bada umarnin tura dakaru 6,000 domin murje 'yan bindiga idan suka ki mika makamansu, Daily Trust ta wallafa.
Gwamnan ya sanar da hakan sa'o'i kadan bayan sarakunan gargajiya sun sanar da shugabannin tsaro da suka ziyarci jihar cewa akwai sama da 'yan bindiga 30,000 dake dajikan jihar.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng