N2.5bn: Ban taɓa damfarar gwamnatin tarayya ba, in ji Zahra Buhari

N2.5bn: Ban taɓa damfarar gwamnatin tarayya ba, in ji Zahra Buhari

- Ƴar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra ta musanta rahoton da Sahara Reporters ta wallafa a kanta

- Sahara Reporters ta wallafa cewa Zahra Buhari-Indimi ta damfari gwamnatin tarayya kudi N2.5bn

- Amma a wasikar da lauyoyin Zahra suka aike wa Sahara Reporters, sun ce sharri ne kuma ita bata taɓa damfara ba

- Lauyoyin Zahra sun bukaci Sahara Reporters ta nemi afuwar Zahra, ta janye rohoton idan ba haka ba ta tafi kotu

Ɗaya daga cikin ƴaƴan Shugaban kasa, Zahra Buhari-Indimi ta ce bata taɓa damfarar gwamnatin tarayya N51bn da N2.5bn ko kuma wani adadin kuɗi ba, The Punch ta ruwaito.

Ɗiyar shugaban kasar ta bayyana hakan ne cikin wasika mai ɗauke da kwanan wata 8 ga watan Maris 2021. Lauyan ta, Nasiru Aliyu (SAN) ne ya saka hannu kan wasikar da ya aike wa kafar watsa labarai ta Sahara Reporters.

N2.5bn: Ban taɓa damfarar gwamnatin tarayya ba, Zahra Buhari
N2.5bn: Ban taɓa damfarar gwamnatin tarayya ba, Zahra Buhari.
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: 'Yar minista da masu garkuwa suka sace da shaƙi iskar ƴanci bayan awanni 48

A cikin wasikar, ƴar shugaban kasar ta zargi Sahara Reporters da "ɓata mata suna" cikin wani rahoto da ta wallafa a ranar 5 ga watan Maris na 2021 mai lakabin "Yadda jigon APC, Danu, shugaban Kwastam ya damfari gwamnatin Nigeria N51bn, ya aika wa ƴar Buhari N2.5bn'.

Rahoton ya yi ikirarin cewa Nasiru Danu ya aike wa yar shugaban ƙasa Buhari N2.5bn cikin N51bn ta asusun gidauniyar ta.

Amma a wasikar da lauyoyin ta suka aike wa Sahara Reporters, Zahra ta ce "babu wani gidauniyarta da aka aike wa irin wannan kuɗin."

Wasikar ta cigaba da cewa duk da cewa ita yar shugaban kasa ne, ita yar kasa ne ta gari mai bin doka da oda kuma bata taba yin damfara ba.

KU KARANTA: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

"Wanda muke karewa ta ce bata damfari gwamnatin tarayya Naira biliyan 51 ko Naira biliyan 2.5 ko wani kudi ba.

"Wanda muke karewa yar kasa ta gari ne mai bin doka, matar aure da mijinta ke ɗaukan nauyin ta."

Lauyoyin sun bayyana rahoton a matsayin karya da ɓata suna Zahra, sun nemi Sahara Reporters ta janye rahoton kuma ta nemi afuwar ta a cikin manyan jaridu uku cikin kwanaki bakwai idan ba haka ba kuma ta garzaya kotu.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel