Wasu Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun shiga tattaunawar sirri da gwamnoni

Wasu Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun shiga tattaunawar sirri da gwamnoni

- Wasu Jiga-jigan PDP sun shiga tattaunawar sirri da gwamnonin ƙasar nan dake ƙarƙashin jam'iyyar

- Abubakar Bukola Saraki, Uche Scondorus na daga cikin waɗanda aka hanga sun shiga taron

- Ana gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar Sokoto dake Asokoro, Babban birnin tarayya Abuja

Kwamitin sasanshi na jam'iyyar APC wanda tsohon shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki yake jagoranta.

Da kuma kwamitin shirye-shirye sun shiga tattaunawar sirri da gwamnonin ƙasar nan waɗan da aka zaɓa karkashin PDP. Jaridar Punch ta ruwaito

KARANTA ANAN: Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi

Har ila yau, daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai membobin kwamitin ayyuka wanda Uche Secondus yake jagoranta.

Ana saran waɗan nan jiga-jigan jami'iyyar zasu tattauna yadda za'a cigaba da tafiyar da jam'iyyar PDP ɗin.

Wasu Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun shiga tattaunawar sirri da gwamnoni
Wasu Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun shiga tattaunawar sirri da gwamnoni Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Taron na gudana ne a gidan gwamnan Sokoto, dake Asokoro, babban birnin tarayyo, Abuja. Ana tsammanin za'a tattauna batutuwa kamar; duba cigaban da aka samu a kwamitin sasanci.

KARANTA ANAN: Buhari Ya Ƙaddamar Da Sabon Ginin Hukumar Raya Yankin Niger-Delta

Za kuma a tattauna hanyoyin da za'a bi wajen sasanta wasu daga cikin shuwagabannin jam'iyyar ta PDP.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai; Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, gwamnan Edo, Godwin Obaseki, gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.

Sauran gwamnonin sune; Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, Gwamnan oyo, Seyi Makinde, gwamnan Benue, Samuel Ortom, da kuma gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwanyi.

A wani labarin kuma Mahukunta sun saka dokar kayyade zancen samari da 'yammata a Kano

Ka'idar zuwa tadi wurin zawarawa ko 'yammatan yankin sau biyu ne a mako daya

Takardar ta samu sa hannun dagacin Tudun Yola inda aka aminta da karfe 5 zuwa 8 na dare a tadin

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel