Mahukunta sun saka dokar kayyade zancen samari da 'yammata a Kano

Mahukunta sun saka dokar kayyade zancen samari da 'yammata a Kano

- Mahukunta a Tudun Yola dake karamar hukumar Gwale sun kayyade lokacin zance a yankin

- Ka'idar zuwa tadi wurin zawarawa ko 'yammatan yankin sau biyu ne a mako daya

- Takardar ta samu sa hannun dagacin Tudun Yola inda aka aminta da karfe 5 zuwa 8 na dare a tadin

Mahukunta a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano sun saka doka ta takaita tadin 'yammata da samari har da zawarawa zuwa kwanaki 2 a mako, Aminiya ta wallafa.

Dokar kayyade wa'adin zancen a mako ta samu sa hannun Dagacin Tudun Yola, Malam Nasidi Hamisu. Ya bayyana karfe 8 na dare matsayin lokacin gama zancen.

Sabbin dokokin wadanda aka gindaya game da zancen zawarawa, samari da 'yammatan sune:

KU KARANTA: Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai

Mahukunta sun saka dokar kayyade zancen samari da 'yammata a Kano
Mahukunta sun saka dokar kayyade zancen samari da 'yammata a Kano. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Takaita yin tadi zuwa ranakun Alhamis da Juma’a kacal.

Lokacin tadi shine karfe biyar na yammaci zuwa takwas na dare.

Budurwa ko bazawara ba za ta yi zance a ko’ina ba sai kofar gidansu.

An haramta kidan DJ, idan kuma ya zama dole, sai da izinin mai garin Tudun Yola da ’yan bangan yankin.

An haramta ta’ammuli da kayan maye ko miyagun kwayoyi a unguwar.

An kuma haramta sayar da kayan maye a daukacin yankin.

Dokar ta hana hira barkatai din wadda ta ce babu sani, ba sabo ga masu karya ta, ta samu goyon bayan jama’ar unguwar da hukumar ’yan sanda, hukumar yaki da sha da fataucin kwayoyi (NDLEA) da ’yan kato da gora da sauransu.

KU KARANTA: Mun baiwa 'yan bindiga buhu 7 na shinkafa don tseratar da rayukanmu, Jami'in kwastam

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin tura dakarun soji 6000 jihar Zamfara. Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da hakan a wata sanarwa da yayi a yammacin Talata, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce da kanshi ya dauki kwanaki hudu a Abuja yana bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki a kan halin da tsaron jihar ke ciki.

"A cikin tattaunawar mu da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan kwamandojin tsaro a Abuja, an yanke shawarar cewa za a tura karin dakaru 6000 jihar domin karawa jami'an tsaron dake jihar karfi."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel