Na tattauna da Gumi, ya yi alkawarin taimaka mana wajen magance matsalar tsaro, NSA Monguno
- Gwamnatin tarayya ta amince Sheikh Gumi ya taimaka mata wajen magance tsaro
- Amma bata bayyana hanyar da babban Malamain zai bi wajen taimakawa ba
- NSA Babagana ya zanna da manema labarai a fadar shugaban kasa
Mai bada shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya bayyana cewa Sheikh Ahmadu Abubakar Gumi, ya yi musu alkawarin taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro.
A hira da manema labarai ranar Alhamis, Monguno, ya ce lallai ya gana da Gumi, kuma yana sauraron yadda Malamin zai taimakawa gwamnati, rahoton TheCable.
Sheikh Gumi ya kasance yana shiga dazuka domin ganawa da yan bindigan yana musu wa'azin ajiye makamai da neman tuba.
Hakan bai yiwa wasu dadi ba inda suke cewa ya kamata gwamnati ta damke Malamin kuma ta bincikesa.
KU KARANTA: Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
KU KARANTA: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar
A cewar NSA Monguno, Gumi dan Najeriya ne kuma yana da hakkin tattaunawa da duk wanda ya ga dama.
"Sheikh Gumi na abinda yake yi ne saboda ya yi imani da haka. Dan Najeriya ne kuma karkashin kundin tsarin mulki zai iya magana da duk wanda ya ga dama," yace.
"Na gana da shi lokacin da muka je Kaduna da hafsoshin tsaro, kuma mun tattauna lokacin zaman kuma ya yi alkawarin taimakawa gwamnati. Muna sauraronsa. Abinda zan iya fadi kenan."
Monguno ya bayyana cewa gwamnati bata fi karfin zama da yan bindigan ba amma ba za ta shiga wani yarjejeniya da wasu mutane marasu gaskiya ba.
A bangare guda, gwamnatin tarayya ta yi watsi da tattaunawar shigo da sojojin haya na kasashen waje don yaki da masu tayar da kayar baya da sauran nau’ikan rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd), ne ya fadi haka a ranar Alhamis yayin wani taron a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce gwamnatin ta gwammace ta yi amfani da dukkanin rundunoni don kawar da yakin.
Asali: Legit.ng