Kwastam sunyi babban kamu, sun kwace kayan 79 miliyan a Kastina

Kwastam sunyi babban kamu, sun kwace kayan 79 miliyan a Kastina

- Hukumar kwastam reshen jihar Katsina ta bayyana cewa tayi ram da kayayyaki da suka kai kimanin 79 miliyan a wata biyu

- Kayayyakin da suka haɗa da buhunan shinkafa, jarkokin mai, motar hawa, motar ɗaukan kaya da sauransu

- Shugaban hukumar reshen jihar Katsina ne ya bayyana haka

Hukumar kula da hana fasakwaurin kayayyaki wato kwastom ta shiyyar Katsina ta bayyana cewa ta cafke wasu kayayyaki masu ɗinbin yawa.

A cewar shugaban hukumar na jihar, kayayyakin zasu kai kimamin 79 miliyan, kuma an kama su ne daga watan Fabrairu zuwa Maris na wannan shekarar.

KARANTA ANAN: Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai

Jaridar PM news ta ruwaito, Mr Adewale Aremu, shugaban hukumar na jihar Katsina ya bayyana hakan ranar laraba a Katsina.

Aremu, yace kayan da aka kwace sun hada da buhunan shinkafa mai nauyin kilo 50 guda 470 wadanda aka boye a waje daban daban a tankar dakon mai.

Kwastam sunyi babban kamu, sun kwace kayan 79 miliyan a Kastina
Kwastam sunyi babban kamu, sun kwace kayan 79 miliyan a Kastina Hoto: @CustomsNG
Asali: Twitter

Shugaban ya ce:

"Sauran kayayyakin sun hada da dilolin gwanjuna guda 327 wanda kudin su yakai 30 miliyan, motar Honda Accord wadda kudin ta sun kai miliyan 8, tare da jarkunan man girki guda 166 waɗanda kudinsu yakai kimanin 1.8 miliyan."

KARANTA ANAN: Za'a fara yiwa mutan Kano allurar rigakafin cutar Korona

"Daga cikin abinda aka kama akwai kwalayen taliya yar waje guda 321, kwalayen couscous 29, kwalayen macaroni 110, kwalayen madara 65, kwalaye 14 na plaster da kuma buhunan sukari guda 187," inji shi

"Tankar mai lambar rajista KWL 427 TH na da kudin aiki 13.5 miliyan. Motar trela da aka dauko kayan gwanjuna na da matsayin naira 12.1 miliyan," a cewar shugaban.

Aremu ya jaddada cewa hukumar kwastam ba zata yi kasa a guiwa ba wajen dakile masu shigo da kaya ba bisa kaida ba cikin kasa, inda yayi nuni da cewa hakan babbar illa ce ga tagomashin tattalin arzikin Najeriya.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun hallaka 25

Sojojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan Boko Haram a artabun da sukayi a karamar hukumar Marte ta jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar Hukumar, wannan artabu ya auku ne ranar Talata, 9 ga watan Maris, 2021.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel